Gwamnonin Kudu maso Yamma na aiki bayan fage domin sako Igboho - Sanwo-Olu

Gwamnonin Kudu maso Yamma na aiki bayan fage domin sako Igboho - Sanwo-Olu

  • Gwamnan Jihar Legas ya ce gwamnonin yankin Yarbawa na kai gwauro da mari wajen ganin an sako Sunday Igboho
  • Ya ce ba lallai ne sai sun fito fili sun bayyana wa jama’a kokarin da suke yi na a sako Igbohon ba
  • An kama Sunday Igboho ne ranar Litinin a filin jiragen sama a Cotonou

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Asabar ya ce gwamnonin Kudu maso Yamma suna aiki ta bayan fage wajen ganin an saki mai ikirarin fafutikar ‘yancin Yarbawa, Sunday Igboho.

An kame Igboho ne a Cotonou na Jamhuriyar Benin ranar Litinin da ta gabata yayin da yake shirin shiga jirgi zuwa Jamus.

Gwamna Sanwo-Olu, wanda ya amsa tambayoyin manema labarai an tambaye shi abin da gwamnonin Kudu maso Yamma ke yi wajen ganin an sako Igboho, rahoton PMNews.

Gwamnan ya amsa cewa da Gwamnonin yankin suna aiki ta bayan fage domin sakin nasa.

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Ya ce gwamnonin ba za su iya zuwa ga jama’a su sanar da abin da suke yi a kan batun Igboho ba.

Gwamnonin Kudu maso Yamma na aiki bayan fage domin sako Igboho - Sanwo-Olu
Gwamnonin Kudu maso Yamma na aiki bayan fage domin sako Igboho - Sanwo-Olu
Asali: UGC

Gwamnan ya kada kuri'arsa a zaben da ke gudana yau

A halin yanzu, Sanwo-Olu ya jefa kuri'a a mazabarsa ta 019, mai lamba 09, Ikoyi a ranar Asabar, yana cewa zaben kananan hukumomin jihar ya kasance cikin lumana ya zuwa lokacin da yake jawabin.

Gwamnan ya isa mazabarsa tare da uwargidarsa, Misis Ibijoke da misalin karfe 11:03 na safe sannan ya kada kuri’a ‘yan mintoci bayan haka.

Ya ce har zuwa yanzu rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, amma ya yi Allah wadai da rashin fitowar masu kada kuri'a a rumfunan zaben.

Sanwo-Olu ya kara da cewa an gudanar da zaben ba tare da matsala ba duk da kalubalen da aka fuskanta tunda farko na makarar jami'an hukumar zaben jihar, LASIEC.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

Yace:

“Mun duba rumfunan zabe guda hudu a kewayen yankin nan, ba zan ce akwai cikowar jama’a ba, amma abubuwa na tafiya lami lafiya.
”Rahoton da aka samu shi ne cewa komi na tafiya lami lafiya sai dai dan jinkirin da jami’ai suka yi na fitowa a makare,”.

Sanwo-Olu ya ce kyan mulkin dimokoradiyya shi ne mutane su bayyana ra’ayinsu a fili ta hanyar akwatin zabe.

Ya jadadda bukatar kara ilimantar da mutane kan bukatar amfani da ‘yancinsu a koyaushe ta hanyar jefa kuri’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel