Masu gasa burodi da sauran harkokin kasuwanci N100,000 saboda amfani da janareto
- Majalisar Kwaryar Abuja za ta fara karbar harajin N100,000 daga ‘yan kasuwa
- An yiwa wannan kudi lakabi 'kudin izinin fitar da hayakin Janareta'
- Harkokin Kasuwancin da ke amfani da janareta da injina lallai sai sun samu izinin aiki
An sanar da masu yin burodi da bankunan kasuwanci da kuma karin wadansu ‘yan kasuwa a Abuja cewa daga yanzu ana bukatar su fara biyan kudin izinin fitar da hayaki wanda zai ci su N100,000.
Za a biyan tarar ga Majalisar Karamar Hukumar Abuja AMAC.
Majalisar ta yi barazanar cewa za a hukunta duk wani dan kasuwa da bai samu wannan izinin ba.
Karamar Hukumar birnin tarayyar ta bayyana cewa:
"Shugabannin Hukumar Kula da Muhalli ta Hukumar Kula da Yankin Karamar Hukumar ta Abuja (ESD), na son sanar da ku harajin Hukumar Kula da Yankin izinin fitar da hayaki mai gurbata muhalli."
Sabuwar dokar ta maida hankali kan harkokin kasuwanci masu amfani da janareta da masu harkokin haka da masu kayan gini da kayan masarufi wadanda ke fitar da iskar gas mai gurbata iska da ruwa da muhalli a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
AMAC ta kafa hujja da kundin tsarin mulki
Majalisar ta bayyana cewa kundin tsarin mulki ya bada daman karban haraji bosa sashe (2C) karkshin hakkokin kananan hukumomi da kuma hukumar kare muhalli (FEPA).
"Dokar ta baiwa majalisar karamar hukuma karfin wajabtawa da karban kudin haraji don kare lafiya muhalli a sashe na (18), (20), (21), (26) da 27.
Asali: Legit.ng