Fim din batsa a arewa: Daya daga cikin 'yammatan faifain bidiyon ta kashe kanta

Fim din batsa a arewa: Daya daga cikin 'yammatan faifain bidiyon ta kashe kanta

Tashin hankali da tashin-tashina sun barke bayan wani mutum mai suna Emeka ya saki wasu bidiyo na batsa da ya nada na wasu 'yan mata da matan aure da ke Jos, jihar Filato.

An gano cewa mutumin na zama ne a yankin Rayfield da ke Jos. An zarge shi da ba wa matan dubu talatin-talatin sannan yayi lalata dasu tare da nadar bidiyon.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, tuni bidiyon wannan abu ya yawaita a jihar. Daya daga cikin matan da aka yi bidiyon da ita kuwa ta kashe kanta bayan yaduwar shi.

Rahoton ya bayyana cewa Emeka yayi wa matan alkawarin biyansu N100,000 duk shekara.

Daya daga cikin matan wacce tayi hira da jaridar Daily Trust kuma ta bukaci a boye sunanta ta ce wata mata ce ta sameta a wajen shakatawa a kan cewa suna bukatar mata masu irin surarta don fitowa a wani fim kuma za a biya su sosai.

Majiyar wacce ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin wadanda abin ya faru da ita, tace sun je tare da kawarta wajen kuma aka karbesu tare.

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a

"Matar da ta kaimu an bata naira dubu ashirin saboda kaimu da tayi. Na jira a wani daki tare da matar a lokacin da kawata suke yi da Emeka kuma ana nadar bidiyon kafin a zo kaina.

"Daga nan sai muka kwana a otal din saboda dare yayi amma da safe kowa ya watse," in ji ta.

Ta kara da cewa lamarin ya faru ne kusan shekara daya da ta gabata kuma Emeka ya yi alkawarin biyansu dubu dari duk shekara. Hakazalika ya bukaci su cigaba da kawo 'yan mata don wannan harkar.

Budurwar ta ce tun bayan sakin bidiyon, ta fara samun matsaloli da 'yan uwanta kuma saurayinta na gudunta.

A yayin mayar da martani a kan aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tyopev Terna ya ce rundunar ta ji jita-jitar al'amarin amma babu wanda ya garzayo don kawo musu rahoto.

Ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da kada su ji kunya ko tsoro, su garzayo don kawo kokensu don a bincika tare da daukan matakin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Jos