Shugaba Buhari ne kadai zai ce mani in yi, kuma in yi – inji Festus Keyamo

Shugaba Buhari ne kadai zai ce mani in yi, kuma in yi – inji Festus Keyamo

Karamin ministan kwadago da samar da aikin yi na Najeriya, Festus Keyamo (SAN) ya zargi wasu ‘yan siyasa da bai ambaci sunansu ba da yunkurin kawo masa cikas a wurin aiki.

Festus Keyamo ya ce wadannan ‘yan siyasa su na yi masa barazana game da tsarin da gwamnati ta kawo na daukar matasa 774, 000 da za su rika yin ayyuka na musamman a fadin kasar nan.

Ministan ya bayyana cewa ba zai biyewa wannan barazana da ake yi masa ba, ya sha alwashin ganin ma’aikatarsa ta yi abin da ya dace na zakulo mutanen da za su yi aiki da gwamnati.

Jaridar Punch ta rahoto ministan ya na bayyana wannan ne a lokacin da ya kaddamar da shugabannin kwamitin jihohi da aka ba alhakin zaben matasan da su ka cancanta da aikin.

Keyamo ya ja kunnen shugabannin da aka nada, da su tsaya su sauke nauyin da ke kansu, domin kowa ya samu damar aikin wucin-gadin da gwamnatin tarayya.

Mai girma ministan ya ce duk shugaban kwamiti da aka samu ya sabawa ka’ida, zai rasa kujerarsa. Gwamnati za ta ba matasa 774, 000 aikin N20, 000, za a shafe watanni uku ana aikin.

“Akwai yunkuri da ake yi mani na barazana a kan wannan tsari, ta yadda za mu biyewa ‘yan siyasa, kuma na ce ba za a yi hakan ba – muddin ina kan kujerar nan.” Inji Keyamo.

KU KARANTA: An dakatar da batun karin kudin wutar lantarki

Shugaba Buhari ne kadai zai ce mani in yi, kuma in yi – inji Festus Keyamo
Festus Keyamo SAN Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Ministan ya cigaba da cewa: “Ina da nasaba; ina da inda na ke aiki; na san daga inda na fito. Kafin in karbi kujerar gwamnati, ina da inda na fito da abin da aka san ni a kai.”

Ya ce: “In ban da shugaban kasa, wanda ya bani wannan babbar damar yi wa gwamnati aiki da kawo wannan tsari, idan har ba shi ya dakatar da ni ba, babu wani ‘dan siyasa da zai iya taka mani burki.”

Keyamo ya ce: “Mutum daya kurum zai iya bani umarni.” A cewarsa kuma wannan shi ne shugaban kasa.

A baya wasu sun rika damka nauyin irin wannan shiri a hannun ‘yan siyasa wanda su ka bata tsarin da alfarma. Wannan karo, ministan ya ce ba zai bari ayi irin wannan ta'adi ba.

“Kafin in zo nan yau, wasu shugabannin siyasa sun yi kokarin cewa sai na je wurinsu, mun sa labule domin a ji wadanda za a ba wannan aiki, na ce masu ba za ayi haka ba.”

Ya fadawa shugabannin cewa: “Ka da ku je gidan kowane ‘dan siyasa ayi taro, ku yi aikinku a ofishin NDE, ka da ku je gidan gwamnati wajen kowa a kan zaban wadanda za su yi aikin.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel