Kasashen Duniya 7 za su ba Najeriya gudumuwar Naira Biliyan 180 a kashe a Arewa maso gabas
- Kungiyar Kasashen G7 ta sha alwashin ba Najeriya tallafin wasu makudan kudi
- Kasashen su na kokarin magance matsalar karancin abinci a Arewa maso gabas
- Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar jikkata miliyoyin mutane a yankin Arewa
‘Yan kungiyar G7 na kasashen da su ka fi cigaba, sun yi alkawarin taimaka wa gwamnatin tarayya da kudi da nufin magance matsalar yunwa.
Jaridar The Cable ta ce wadannan kasashen bakwai sun yi alwashin bada gudumuwar fam Dala miliyan 382 domin a kawo karshen karancin abinci.
Kasashen sun bayyana wannan wajen kaddamar da shirin 'G7 Famine Prevention Compact Launch’ a jiya ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2021.
KU KARANTA: Abin da ya hana rikicin Boko Haram kare wa har yau - Minista
Za ayi amfani da wannan makudan kudi ne a Arewa maso gabashin Najeriya inda mutane su ke cikin mawuyacin hali a dalilin rikicin Boko Haram.
Kasashen kungiyar G7
Kasashen G7 sun kunshi; Amurka, Birtaniya, Kanada, Faransa, Jamus, Italiya da Jafan. Kasashen nan sun fi kowa karfin tattalin arziki a fadin Duniya.
Idan aka yi lissafi da darajar Naira ta gida, wannan gudumuwa ta kai kimanin Naira biliyan 190.
Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta karanto jawabi a madadin kasashen, inda ta ce sun ware wa kasashe 42 gudumuwar Dala biliyan bakwai.
KU KARANTA: Ba za mu kyale 'Yan ta'adda ba - Buhari
Ana fuskantar matsala a Arewa maso gabashin Najeriya
Jaridar nan ta Punch ta rahoto kasashen su na cewa sun damu da halin da mutanen na Arewa maso gabas su ke ciki, don haka su ka kawo masu agaji.
“Mun damu sosai a kan halin da Bil Adama su ke ciki a Arewa maso gabas. Mutane miliyan 8.7 su na bukatar taimako, an jikkata mutane miliyan 1.9.”
“Saboda haka mu na ganin cewa za a iya fuskantar matsalar karancin abinci mai kyawu da yunwa.”
A jiya ne ku ka ji cewa Mai girma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya damu da mawuyacin halin da masu gudun hijira su ke ciki.
Baya ga mugun talauci, ana yawan haihuwan yara rututu a sansanin IDPs da ke Jihar Borno. Umara Zulum ya ce ana kuma fama da matsalar shan kwaya.
Asali: Legit.ng