Babu ruwanmu: Ba a Ingila aka yi ram da Nnmadi Kanu ba inji Gwamnatin Birtaniya

Babu ruwanmu: Ba a Ingila aka yi ram da Nnmadi Kanu ba inji Gwamnatin Birtaniya

  • Kasar Birtaniya ta yi magana bayan an kama Nnmadi Kanu a ketare
  • Gwamnatin kasar Turan ta ce ba a cikin Ingila ne aka cafke Kanu ba
  • Shugaban kungiyar ta IPOB ya na da takardar zama ‘Dan kasar Ingila

Kasar Birtaniya ta yi magana game da cafke shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnmadi Kanu da aka yi, Daily Trust ta fitar da wannan rahoto dazu.

A ranar Talata, 29 ga watan Yuni, 2021, ofishin jakandancin Birtaniya ta ce ba a Ingila aka kama Nnmadi Kanu, wanda aka dade ana neman ram da shi ba.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN ya bada sanarwar kama Kanu, ba tare da ya yi cikakken bayani ba.

KU KARANTA: Abin da ya sa na tsere daga Najeriya - Kanu

Da yake jawabi, Abubakar Malami ya ce Kanu ya shiga hannun hukuma ne a sakamakon kokarin da jami’an tsaron Najeriya da masu leken asiri su ka yi.

Ganin cewa tun da shugaban kungiyar ta IPOB mai fafutukar samar da kasar Biyafara ya tsere daga Najeriya, ya na Ingila, an yi tunani a can aka kama shi.

Nnmadi Kanu ya na da takardar kasar Ingila

Kamar yadda Kanu ya ke mutumin Najeriya, rahoton ya ce haka zalika ya na da takardar zama ‘dan kasar Birtaniya, don haka Ingila ma gida ce a wurinsa.

Mai magana da yawun bakin ofisihin jakadancin Birtaniya, Mista Dean Hurlock, ya shaida wa jaridar The Cable cewa ba a cikin Ingila aka cafke Kanu ba.

Nnmadi Kanu
Mazi Nnmadi Kanu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Kotu ta amince hukumar DSS ta cigaba da tsare Nnamdi Kanu

“Mun tabbatar da cewa ba a Ingila aka cafke Nnamdi Kanu, aka dawo da shi kasarsa ba.”

Dean Hurlock ya tabbatar da wannan a madadin gwamnatin kasar.

A wani kaulin, an cafke Nnamdi Kanu ne a kasar Brazil, inda aka shirya masa tarko da wata mata wanda ta ke aiki da jami’an tsaro, amma ta yi masa basaja.

Wannan Baiwar Allah ta shirya za su hadu da Kanu a wani otel, ko da ya shigo daki sai aka kama shi, daga nan aka yi masa allura, sai aka dawo da shi Najeriya.

Kun ji cewa Malami ya tabbatarwa manema labarai mai cewa an kama Kanu a ranar Lahadi 27 ga watan Yuni, kuma an dawo da shi Nigeria ya fuskanci shari'a.

Hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron na kasa da y'an sandan kasa da kasa na Interpol su ka raka rawar gani wajen kama wannan mutumi da ake ta nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng