Lauyan Nnamdi Kanu ya bada tabbacin za a fito da shi kwanan nan, ya ce ba za a iya daure shi ba
- Ifeanyi Ejiofor ya ce mutane su dage da addu’a domin a fito da Nnamdi Kanu
- Lauyan ya ce Kanu ba zai dade ba, zai samu ‘yanci daga tsarin da aka yi masa
- An hana Shugaban na IPOB hadu wa da iyalinsa ko ya ga Likitansa inji Ejiofor
Barista Ifeanyi Ejiofor wanda shi ne lauyan da yake kare shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya yi magana game da tsare shi da ake yi a Najeriya.
Ifeanyi Ejiofor ya shaida wa manema labarai cewa kwanan nan za a fito da Nnamdi Kanu daga tsari.
Jaridar The Nation ta rahoto lauyan ya na cewa babu kwararan hujjojin da gwamnati ta ke da su da za su iya gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban kuliya.
KU KARANTA: Matasa sun ce a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa
A kara hakuri, ayi ta addu'a - Lauya
Lauyan ya yi kira ga mutanen Biyafara su cigaba da yi wa Nnamdi Kanu addu’a, sannan su kara hakuri da halin da jagoran kungiyar na IPOB ya shiga.
“Mu na da yardar cewa Mazi Nnamdi Kanu zai fito ba da jima wa ba, kafin lokacin da mu ke tunani, kuma zai fito lafiya kalau.”
“A jefi mutum da zargin aikata laifi dabam, sannan a iya tabbatar da laifin a kotu dabam. Amma ina tunanin ba su da wata hujja mai karfi da za ta iya sa a daure shi.”
Jikin Nnamdi Kanu ya fara murmurewa
Sahara Reporters ta ce Ejiofor ya ce Kanu ya na samun lafiya duk da muzguna masa da aka yi yayin da ake tsare shi a kasar Kenya, a cewarsa ya na samun sauki.
KU KARANTA: Gwamna ya kalubalanci Buhari a kan cafke Nnamdi Kanu
“Babu abin damu wa a kai. Jikinsa na samun sauki. Sai dai an hana shi ganin iyalinsa, musamman mai dakinsa da ‘ya ‘yansa, wannan ma muzguna wa ce."
“Mu na yin duk abin da za mu iya domin ganin an koma tsare shi a wurin da ya dace zuwa lokacin da za a fara shari’a. Mu na kokarin samun likitoci su duba shi."
Jaridar ta rahoto Ifeanyi Ejiofor ya na cewa babu abin da zai hana shi kare Nnamdi Kanu a kotu, ya ce babu wata barazanar da za ta yi aiki a kansa, ba ya shakkar kowa.
A baya kun ji Majalisar Birtaniya ta shirya zama domin tafka muhawara kan yadda aka dawo da shugaban kungiyar na IPOB, Nnamdi Kanu, Najeriya daga kasar Kenya.
Asali: Legit.ng