Ana yawan lalata da ‘Yan mata a sansanin gudun hijira, ana haihuwan yara inji Gwamna Zulum

Ana yawan lalata da ‘Yan mata a sansanin gudun hijira, ana haihuwan yara inji Gwamna Zulum

Gwamna Babagana Umara Zulum ya koka kan matsalar lalata da shan kwaya

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce wannan sun yawaita a sansanonin IDPs

Gwamnan ya na kokarin ganin mutane sun koma gidajensu, su cigaba da noma

Mai girma gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damu wa game da matsalar lalata da shan kwayoyi da ake yi a sansanin gudun hijira.

Jaridar Daily Trust ta ce Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a shirin Sunrise Daily da ake yi a gidan talabiji.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya zanta da manema labarai ne a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021.

KU KARANTA:

Babagana Zulum ya ce jihar Borno ta na fama da yawan zinace-zinace da kuma amfani da miyagun kwayoyi tsakanin mutanen da ke tsare a sansunan IDP."
“Dole mu shawo kan matsalolin zamantake wa, siyasa da na tattalin arzikin da rikicin suka zo da su, ya na da muhimmanci saboda karuwar talauci a yankin.”
“Wannan abu ne da zai ta'azzara rashin tsaro da ya shafi karancin abinci a yankin nan, domin rashin wadataccen abinci shi ne mafi munin matsalar tsaro.”
“Shiyasa gwamnatin jihar Borno a karkashin shugabancina ta dage kan wayar da kan mutane su koma gona, manoma su koma goakinsu, su samu amfani.”
Babagana Umara Zulum
Farfesa Babagana Umara Zulum a IDPs Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC ta na neman Mukarrabin Gwamnan Sokoto ya yaudari 'yan kasuwa

“Ba zai yiwu kungiyoyi su yi ta kai abinci da sauran kaya ga mutanenmu da ke zama a sansanin gudun hijira ba, Dole ne mutane su nemi abin da za su ci.”
“Gaskiya mun yi kuskure, mun tara mutane da yawa a sansanin IDP, wannan ba daidai ba ne. Ana samun yawaitar zina da shan kwayoyi a sansanonin na IDPs.”

Gwamna Zulum ya ce a dalilin wannan, ana ta haihuwar yara barkatai, ya bukaci gwamnati ta yi abin da ya dace domin a maida mutane inda su ka fito a cikin mutunci.

Kungiyar Arewa ta NEF ta fadi sharadin ta na goyon bayan mutanen Kudu su karbi mulki bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adinsa a zaben 2023.

Kakakin NEF, ya ce ba haka kurum za a sa Arewa ta zabi ‘Dan Kudu ba, sai an gamsar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel