Ministan Buhari ya fadi abinda ya hana rikicin Boko Haram kare wa

Ministan Buhari ya fadi abinda ya hana rikicin Boko Haram kare wa

- Sadiya Umar Farouq, ministar Buhari ta zargi rashin alaka mai kyau a tsakanin rundunar soji da kungiyoyi masu zaman kansu a matsayin abinda ya hana ganin nasarar da ake samu a yaki da Boko Haram

- Ministar ta bayyana hakan ne a wurin bude wani taro na kwanaki uku na hadin gwuiwa da jami'an tsaro da kungiyoyi masu zaman kansu da aka fara a Maiduguri, babban birnin jihar Borno

- Rundunar soji ta zargi wasu kungiyoyi biyu masu zaman kansu da taimako tare da goyon bayan harkokin kungiyar Boko Haram a jihar Borno

Ministar taimakon jama'a da kiyaye afkuwar annoba, Sadiya Umar Farouq, ta dora alhakin rashin karewar rikicin Boko Haram a kan rashin kyawawan dabaru da kulla alaka mai kyau bangaren rundunar soji da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da ke yankin arewa maso gabas.

Uwargida Sadiya ta bayyana hakan ne a wurin bude wani taro na kwanaki uku na hadin gwuiwa da jami'an tsaro da aka fara a ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ministar ta bayyana cewa duk da cewa kowanne bangare yana iyakar kokarinsa domin ganin an kawo karshen rikicin Boko Haram, "amma rashin kulla hulda ta fuskar tsaro ta hana nasarar da ake samu ta bayyana."

DUBA WANNAN: Yanzu - Yanzu: Maina ya bayyana a kotu kan keke guragu

Sadiya ta alakanta dakatar da wasu kungiyoyi biyu masu zaman kansu; 'Action Against Hunger' da 'Mercy Corps', da rundunar soji ta yi a jihar Borno, da rashin kulla alaka mai kyau domin yn aiki tare a filin daaga.

Tuni kungiyar 'Mercy Corps, da 'Action Against Hunger' suka koma bakin aiki bayan rundunar soji ta janye dakatarwar wucin gadin da aka yi musu a cikin makon da ya gabata.

Rundunar soji ta zargi kungiyoyin biyu da taimako tare da goyon bayan harkokin kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel