Bayan tunbuke Muhuyi, Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar yaki da rashawan Kano

Bayan tunbuke Muhuyi, Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar yaki da rashawan Kano

  • Gwamnan Kano ya nada sabon shugaban hukumar amsa korafe-korafen jihar
  • Hukumar ke da hakkin yaki da cin hanci da rashawa a fadin jihar
  • Jihar Kano na daya daga cikin jihohin Najeriyan dake da irin wannan hukumar

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin Mahmoud Balarabe a matsayin mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawan jihar Kano watau PCACC.

Wannan ya biyo bayan dakatad da Muhyi Rimingado, wanda ya rike mukamin na tsawon shekaru shida.

Wannan ya bayyana ne a jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar, ya saki, rahoton DailyNigerian.

Yace:

"Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya amince da nadin Barista Mahmoud Balarabe, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar amsa korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano.
"Zai kama aiki ba tare da bacin lokaci ba kuma an umurcesa ya gudanar da aikinsa bisa dokokin hukumar."

DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota

Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar yaki da rashawan Kano
Bayan tunbuke Muhuyi, Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar yaki da rashawan Kano Hoto: Dr Abdullahi Ganduje
Asali: UGC

KU KARANTA: Abin mamaki yayin da wani mutum ya kara aure da kudin tallafin da kungiya ta ba shi domin kula da ’ya’yansa 7

A jihar Kano kadai ake yaki da rashawa kamar EFCC da ICPC, Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Alhamis ya bayyana cewa a jihar Kano kadai ake yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda gwamnatin tarayya ke yi.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin rantsar da kwamitin tafiyar da dabarun yaki da rashawa na hukumar korafe-korafe da yaki da rashawan jihar Kano.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce wannan ce kwamiti mafi muhimmanci da za'a rantsar kan yaki da rashawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel