Sace daliban Kaduna: Yadda aka kashe sojan ruwa wata uku bayan aurensa
- Sojoji biyu ne suka mutu yayin kokarin kare daliban lokacin da masu garkuwar suka dira makarantar
- Dukkan sojojin biyu kurata ne daya sojan ruwa guda kuma sojan kasa
- Harin da ’yan bindigar suka kai shi ne na hudu inda suka sace dalibai a Jihar Kaduna tun watan Disamban bara
Sojan Ruwan Najeriya, Bilal Mohammed, wanda ya mutu a lokacin da yake kare daliban makarantar Baptist High School da ke Jihar Kaduna, wadanda ’yan bindiga suka sace, ya yi aure a watan Afrilun nan.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa sojan, mai mukamin kurtu ya mutu ne tare da wani sojan Najeriya, Salisu Rabiu, yayin da suke yin arangama da 'yan ta'addan da suka kai hari makarantar inda suka yi awon gaba da dalibai 150 a safiyar ranar Litinin.
Jaridar, a ranar Talata ta bayar da bayanan sojojin biyu da wadansu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne suka kashe a lokacin da suka kai hari makarantar sakandare a Maramara da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
A ranar Litinin ne wadasu ’yan bindiga suka far wa makarantar da ke wajen garin Kaduna, inda suka kwashe sama da dalibai 150.
DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota
KU KARANTA: Wani mutum ya kara aure da kudin tallafin da kungiya ta ba shi domin kula da ’ya’yansa 7
‘Yan bindigar sun kuma harbe sojojin biyu inda suka mutu take.
"Wani jami'in Sojan Najeriya, Salisu Rabiu mai mukamin kurtu da na sojan ruwa shi ma kurtu Bilal Mohammed barayin daji sun hallaka su a yayin harin," kamar yadda wata majiya ta shaida wa Sahara Reporters.
Harin na ranar Litinin a kan makarantar Bethel Baptist High School shi ne karo na hudu da ake sace daliban makaranta a cikin garin Kaduna tun watan Disamba.
Sace-sacen dalibai ya yawaita a Arewacin Najeriya
Lamarin ya zo 'yan makonni bayan wadansu ’yan bindiga sun sace wadansu daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin-Yauri.
A ranar 30 ga Mayu, an sace daliban makarantar Islamiyya da ke Tegina, a cikin Jihar Neja.
A ranar 12 ga Maris, barayin sun kuma sace dalibai 39 na Kwalejin Koyon Gandun Daji da ke Afaka a karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.
A watan Fabrairun 2021, wadansu ’yan bindiga sun kai hari a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kagara cikin Jihar Neja, inda suka yi awon gaba da daliban makarantar da ma malamai da kuma ma’aikata.
Haka nan a ranar 11 ga watan Disamban 2020, an kuma sace ’yan makarantar sakandare guda 344 a Kankara da ke Jihar Katsina, mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, yayin da yake can.
Asali: Legit.ng