Me ya sa za a kama Nnamdi Kanu sannan a kyale Sheikh Gumi da barayin daji? – Wani Gwamna ya kalubalanci Buhari
- Gwamnan Jihar Bayelsa Douye Diri ya ce ya rasa fahimtar azancin kama Nnamdi Kanu alhali aka bar Sheikh Gumi yana yawo
- Gwamna Diri ya nunar da cewa Gumi ya zama mutumin da babu wanda ya isa ya nuna masa yatsa, yana mai cewa babu adalci sam a hakan
- Sannan ya koka da yadda gwamnatin Buhari take ci gaba da zura wa barayin daji suna aika-aika a fadin kasar nan
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sanya ayar tambaya kan dalilin da ya sa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kama jagoran haramtacciyar kungiyar masu neman ballewa ta Biafra (IPOB), wato Nnamdi Kanu, sannan a daya gefen ba ta kama fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ba, kan zargin sa da alaka da 'yan bindiga.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata, a cikin wani shirin gidan telebijin na Channels, mai suna Sunrise Daily, inda ya ce ya lura cewa Gumi ya zama wani mutum da babu mahalukin da ya isa ya taba shi, inda ya ce hakan ai rashin adalci ne.
Gwamna Diri ya ce:
“Abu biyu ne zan fada a nan: na farko dai, ya kamata a yi wa Nnamdi Kanu shari’ar adalci ta yadda kowa da kowa musamman ’yan kabilar Ibo ba za su ga cewa an masa zalunci ba.
“Na biyu, yayin da muke magana game da kungiyar IPOB, me za a ce game da ’yan bindiga da makiyaya da ke aikata kashe-kashe a yankin Arewaci da ma a sauran sassan kasar nan? Ina kuma batun Sheik Gumi? Ya zama wani mutumin da babu mahalukin da ya isa ya daga masa yatsa. Wannan rashin adalci ne sosai."
DUBA NAN: Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed
KU KARANTA: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya
Gumi ya bukaci a yafewa yan bindiga
Gumi a baya-bayan nan ya gargadi gwamnati game da kashe 'yan bindigar, yana mai cewa suma ana kuntata musu ana kuma zaluntar su.
Malamin ya nace kan cewa babu wata makaranta da za ta zauna lafiya a yankin Arewa maso Yamma har sai lokacin da gwamnati ta tattauna da 'yan bindigar.
Bayanin nasa na baya bayan nan ya haddasa yamutsa gashin baki kan zargin sa da hannu a aika-aikar ‘yan bindigar da ma dalilin da ya sa gwamnatin Shugaba Buhari ta kasa neman sa domin yi masa tambayoyi.
Jaridar Legit a ranar 29 ga Yuni ta ruwaito Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yana zayyana zarge-zargen da ake yi wa Nnamdi Kanu, yana mai cewa dole ne ya ci gaba da fuskantar shari’ar da ake masa a kotu nan da nan.
Asali: Legit.ng