A yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, kungiyar Matasan Kano ga gwamnatin tarayya
- Kungiyar Matasan Kano Masu Rajin Wayar da Kai ta yi martani kan kame jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
- Kungiyar ta zayyana wasu daga cikin miyagun laifukan da Kanu ya ingiza a Najeriya yayin da ya gudu zuwa kasashen waje
- Sai ranar 26 ga watan Yuli aka tsara ci gaba da shari’ar jagoran IPOB a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja
Wata kungiyar rajin wayar da kai da ke a Kano mai suna Kungiyar Matasan Kano Advocacy Organization (KMKAO), ta bukaci kotunan Najeriya da su yanke hukuncin kisa kan jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Juma’ah a shafin Facebook ta zargi Kanu da alhakin kisan dubban rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.
Shugaban kungiyar, Alhassan Haruna Dambatta, ya ce ya kamata jagoran na IPOB ya fuskanci hukuncin kisa saboda zargin sa da aikata ta’addanci.
Kungiyar ta ce: '
'Ko shakka babu Kanu da ire-irensa sun nuna cewa su ‘yan wutar jahannama ne inda can ne ya kama ce shi da zai tarar da takwarorinsa suna fuskantar hukuncin Allah.
“Ya dace a saka shi cikin buhu sakamakon yadda ya tsara ya jagoranta ya kuma samar da kudaden aikata ta’addancin da ya salwantar da rayukan dubban ‘yan Najeriyar da ba su ji ba gani ba wadanda laifinsu kawai shi ne sun yi da’a da Kundin Mulkin Kasa da ya ba su damar watayawa da ma zama inda ransu yake so.”
Kungiyar ta yi ikirarin cewa ya kamata jagoran na IPOB ya fuskanci hukunci mai tsanani saboda zargin tunzura husumar kashe mutane tare da kone dukiyoyinsu.
A cewar jaridar Daily Nigerian, kungiyar ta yi zargin cikin wata hudu ya yi kira tare da kitsa munanan hare-hare guda 55 ko dai a kan jami’an tsaro ko kuma fararen hular da ba su san hawa ko sauka ba a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
Kamar yadda ka kama Kanu, ka kama shugabannin Miyetti Allah, Ortom ga Buhari
A bangare guda, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kama Fulani makiyaya masu yawo da bindiga ballantana shugabannin Miyetti Allah kamar yadda ya kama shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Ortom wanda ya bayyana cewa a kasar ketare aka cafko Kanu, ya zargi cewa Miyetti Allah ce ke aiwatar da miyagun hare-hare a jihar Benue.
Asali: Legit.ng