Shugaban kasa Buhari ya yi nadin mukami, ya nada sabon Jakada a kungiyar WTO
- Adamu Mohammed Abdulhamid zai dare kujerar Jakadan Najeriya a WTO
- Fadar Shugaban kasa ta bayyana wannan ne a wata takarda da COS ya fitar
- Ministan kasuwanci, Niyi Adebayo, ya ce Jakadan ya yi shekaru 28 a WTO
Shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Dr. Adamu Abdulhamid a matsayin Jakadan Najeriya zuwa kungiyar kasuwancin Duniya na WTO.
Mai girma shugaban kasar ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar daga ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.
Farfesa Ibrahim Gambari ya rubuta wa Ministan masana’antu, kasuwanci da zuba hannun jari na kasa, Niyi Adebayo, wasika inda ya sanar da shi a kan nadin.
KU KARANTA: Wani ‘Dan Majalisar Ingila zai bijiro da batun Nnamdi Kanu a Birtaniya
Shugaban Najeriya ya fitar da jawabi da ya yi wa take da ‘PMB ya nada sabon Jakadan Najeriya zuwa WTO”, wanda ma’aikatar kasuwanci ta fitar a dazu.
Kamar yadda jaridar Punch ta bayyana mana, jawabin ya fito ne daga bakin babban sakataren ma’aikatar kasuwanci da masana’antu da zuba hannun jari.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr. Adamu Mohammed Abdulhamid a matsayin sabon Jakadan Najeriya zuwa kungiyar WTO.”
Dr. Abdulhamid zai yi shekara hudu a kan wannan kujera da ke garin Geneva, a kasar Switzerland.
Niyi Adebayo, ya yi kira ga Adamu Mohammed Abdulhamid ya yi aiki tare da shugabar kungiyar, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala da sauran kungiyoyin kasar waje.
KU KARANTA: Ana so a haramtawa ‘Yan siyasan da suka haura shekaru 60 takara
"Mai girma Ministan ya ba sabon Jakadan shawarar ya hada-kai da kungiyoyin Duniya irinsu; United Nations Conference on Trade and Development, International Trade Centre, da World Intellectual Property Organization, domin cigaban Najeriya."
Wanene Adamu Mohammed Abdulhamid
Punch ta ce Dr. Adamu ya rike kujerar Chargé d’ Affaires na kasar Najeriya a WTO kafin yanzu.
Sabon jakadan ya na da digiri a ilmin tattalin arziki da kasuwanci daga wasu jami’o’in kasar waje, sannan ya yi PhD a fannin huldar kasashen waje a kasar Ingila.
Har ila yau, Adamu ya shafe shekaru 28 ya na aiki a kungiyar WTO a matsayin jami’in kasuwanci, shi ne ya taya Dr. Okonjo-Iweala yakin zama shugabanar WTO.
Asali: Legit.ng