Da dumi-dumi: Duk da adawar PDP, kwamitin Majalisar Dattawa ya fara tantance Lauretta Onochie
- Yau ne aka fara zaman tantance nada Lauretta Onochie a Majalisar Dattawa
- Shugaba Buhari ne ya aika sunanta domin nada ta mukamin
- Hadimar Fadar Shugaban Kasa ce
Kwamitin Zauren Majalisar Dattawa kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ya fara zaman tantance hadimar fadar Shugaban Kasa wato Lauretta Onochie, domin nada ta Kwamishinar hukumar zaben.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya aika sunan Lauretta Onochie domin ba ta mukamin Kwamishinar Hukumar zaben mai zaman kanta.
DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota
PDP tayi zanga-zanga
Daily Trust ta fitar da rahoto cewa a yau ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, 2021, wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, sun shirya zanga-zanga a majalisar tarayya.
‘Yan jam’iyyar adawar sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne domin nuna rashin amincewarsu a kan shirin ba Misis Lauretta Onochie mukami.
Onochie ta na cikin masu taimaka wa shugaban Najeriya wajen harkar yada labarai ta kafafen zamani.
Asali: Legit.ng