Idan zaben 2023 ta zo, mu hadu a rumfar zabe kurum – Dattawan Arewa ga Gwamnonin Kudu

Idan zaben 2023 ta zo, mu hadu a rumfar zabe kurum – Dattawan Arewa ga Gwamnonin Kudu

  • Kungiyar NEF ta maida martani a kan matsayar Gwamnonin Kudancin kasar nan
  • Dattawan Arewa sun ce babu wanda ya isa ya sa su saryar da damarsu a zaben 2023
  • Hakeem Baba-Ahmed ya ja kunnen Gwamnoni cewa ba a samu mulki sai da kuri’a

Kungiyar dattawan Arewa ta NEF ba ta gamsu da matsayar gwamnonin kudancin kasar nan, na kai takarar shugaban kasa zuwa Kudu a zaben 2023 ba.

Jaridar Daily Post ta fitar da rahoto kungiyar ta na cewa ba za ta saryar da kujerar da ake samu ta hanyar fitowa a yi zabe, wanda ya yi galaba ya lashe ba.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya fitar da jawabi

Darektan yada labarai da wayar da kai na kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ba za su yarda barazana ta yi aiki a kansu ta kowace irin fuska ba.

KU KARANTA: Mulki 'Yan kudu su ke nema a 2023 - Sanata Adamu

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya na ganin abin da ya dace da gwamnonin kudu shi ne su bari a shiga zabe.

“Tsarin mulkin damukaradiyya mu ke bi, kuma za a tsaida wanda zai zama shugaban kasa na gaba ne ta hanyar mutane su fita, su zabi duk ‘dan takarar da su ka gamsu da shi.”

Baba-Ahmed ya ke cewa gwamnonin kudun da su ka dauki wannan matsaya sun fito ne daga APC da PDP, kuma suna da ta-cewa a wadannan jam’iyyun biyu.

A madadin kungiyar dattawan na Arewa, Dr. Baba-Ahmed ya ba gwamnonin na kudancin Najeriya shawara su sa jam’iyyun su zabi yankin da za a ba takara.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisan PDP 1 tak ya rage a Zamfara bayan Gwamna ya koma APC

Wasu Gwamnonin Kudu a taro
Gwamnonin Kudu a taro
Asali: Twitter

Hakeem Baba-Ahmed yake cewa idan har an yi wannan, sai gwamnonin jihohin kudun su yi kokarin shawo kan mutane daga ko ina su zabi ‘dan takararsu.

Ra’ayin tsohon jigon na jam’iyyar APC shi ne kowane ‘dan kasa ya na da damar da zai zabi duk wanda yake so, ya ce wata barazana ba za ta yi tasiri a nan ba.

Kamar yadda All Africa ta kawo rahoto, Darektan kungiyar ta NEF ya ce ‘yan siyasan yanzu sun lalace, suna ganin za su iya samun mulki a sama da irin haka.

A jiyan kun ji cewa Gwamnonin Jihohin Kudu sun ce 3% da za a ba su idan aka gano danyen mai ya yi kadan, su ka bukaci a koma wa shawarar 5% da ake kanta.

Majalisar Tarayya ce ta rage kason da za a ba jihohin kudun masu arzikin mai daga 5% zuwa 3%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel