Yanzu-Yanzu: An yi wa shugaban kasar Haiti kisar gilla a gidansa
- Gwamnatin kasar Haiti ta bayyana yadda wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe shugaba Jovenel Moise
- Ana fargabar mutuwar Moise na iya kara janyo rabuwar kai a kasar da dama ta dade tana fuskantar rikicin siyasa
- Farai ministan kasar Haiti na wucin gadi, Claude Joseph ya tabbatar da kashe shugaban kasar na Haiti
Hankula sun tashi bayan rahotanni sun bazu na cewa an kashe shugaban kasar Haiti, Jovenel Moise a gidansa da ke babban birnin kasar, Port-au-Prince.
Yahoo News ta ruwaito cewa ofishin Farai ministan wucin gadi na kasar, Claude Joseph ne ta fitar sanarwar kisar Moise.
A cewar sanarwa daga ofishin Claude Joseph, Farai minista na wucin gadi na Haiti, an kashe Moise ne cikin dare a gidansa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Sanarwar ta ce:
"Wasu tawagar mutane da ba a san ko su wanene bane suka kashe shi, wasu daga cikinsu na magana da harshen faransanci."
Sanarwar ta ce an harbi mai dakin shugaban kasar amma ba ta mutu ba.
Yan bindigan sun kutsa gidan Moise misalin karfe 1 na dare a ranar Alhamis.
KU KARANTA: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno
Farai ministan ya bukaci yan kasar su kwantar da hankulansu, yana mai cewa;
"Yan sanda da sojoji suna aiki kan lamarin domin gano wadanda suka yi wannan aika-aikan."
Yan hammaya na zargin Moise da mulkin kama karya
Aljazeera ta ruwaito cewa yan hammaya a Haiti na zargin Moise, wanda ya zama shugaba a 2017 da neman kafa mulkin kama karya da wuce wa'adinsa, zargin da ya musanta.
Yan hamamayar sun ce ya kamata wa'adin Moise na shekaru biyar ta kare a ranar 7 ga watan Fabrairun 2021, shekaru biyar daga ranar da tsohon shugaban kasa Martelly ya sauka daga mulki.
Amma, Moise, ya dage kan cewa yana da sauran shekara daya a wa'adinsa.
Ya kasance yana mulkar kasar da dokokin soji bayan an jinkirta yin babban zaben 2018 sakamakon rikici kan lokacin da wa'adinsa za ta kare.
'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa
A wani labarin daban, Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.
A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.
Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.
Asali: Legit.ng