Damfara: Hukumar EFCC na farautar Hadimin Gwamna Tambuwal kan zargin cin kudin mutane

Damfara: Hukumar EFCC na farautar Hadimin Gwamna Tambuwal kan zargin cin kudin mutane

  • EFCC ta ce ta na zargin Bello Malami Tambuwal da yaudarar masu saida motoci
  • Bello Malami Tambuwal ya ci miliyoyin masu saida motoci da sunan Mai gidansa
  • Wannan mutum na cikin masu ba gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal shawara

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta na neman wani hadimin gwamnan Sokoto, Bello Malami Tambuwal.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, Bello Malami Tambuwal ya na cikin masu ba mai girma gwamna Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal shawara.

EFCC ta bada sanarwar cewa ta na neman wannan mutum ne saboda ana zargin cewa ya na amfani da kujerarsa wajen damfarar masu saida motoci.

KU KARANTA: EFCC ta gurfanar da jami'an gwamnatin Sokoto a kan zargin satar N500m

Jaridar ta rahoto shugaban hukumar EFCC na shiyyar Arewa ta yamma, Usman Kaltungo, ya na wannan bayani a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli, 2021.

Usman Kaltungo ya ce mafi yawan motocin da ake zargin wannan mutumi, Bello Tambuwal ya karba daga hannun dillalai, kirar kamfanin Hyundai ne.

“Ya na zuwa wajen dilallan motoci ya na yi masu karya. Sai ya fada masu cewa gwamna (Aminu Tambuwal) ne yake so ya saya wa wani mota.”
“Bayan ya karbi motar, sai ya saida ta a kasuwa, ya kashe kudin wajen wani abu na dabam.”

KU KARANTA: EFCC ta karbo $100m a hannun tsohon kamfanin Atiku - Bawa

Bello Malami Tambuwal
Bello Malami Tambuwal Hoto: @EFCCNigeria
Asali: Facebook

Rahoton ya ce mai ba gwamnan shawara ya tsere bayan hukumar EFCC ta bada belinsa a baya.

Jami’in na EFCC ya ce kawo yanzu EFCC ta karbe Naira miliyan 1.6 daga hannun Tambuwal, sannan akwai wasu Naira miliyan 2.250 da ke hannunsa.

Kaltungo ya shaida wa manema labarai cewa a yau Alhamis, 8 ga watan Yuli, 2021, ake sa ran za a gurfanar da Malami domin Alkali ya yanke masa hukunci.

A makon nan ne ku ka ji cewa wani Mai sarautar gargajiyan a yankin Miango, a garin Bassa da ke jihar Filato ya sha da kyar a hannun 'yan bindiga a hanyar Jos.

Hakimin na Miango ya dawo daga wani taro da aka yi domin sulhu da ‘Yan bindiga, sai wasu miyagu su kayi masa kwanton-bauna, su ka buda masa wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng