'Yan sanda sun damƙe wani ɗan fashi da sulken sojoji da muggan makamai

'Yan sanda sun damƙe wani ɗan fashi da sulken sojoji da muggan makamai

  • Yan sanda a jihar Bayelsa sun damke wani mutum da ake zargi da fashi da makami a Famgbe a Yenagoa
  • An kama wanda ake zargin dauke da makamai, harsashi, muggan kwayoyi da kuma rigar kare harsashi na sojoji
  • Kakakin yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, cikin sanarwar da ya fitar ya ce wanda ake zargin yana bada hadin kai

Jami'an yan sanda na Operation Puff Adder II ta rundunar yan sandan jihar Bayelsa ta kama wani da ake zargi da aikata fashi da makami.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama Teke Kolokol in dauke da makamai da sulken dakarun sojoji.

DUBA WANNAN: Bethel Baptist: Ƴan bindiga sun nemi a basu shinkafa da wake da zasu ciyar da ɗalibai 121 da suka sace a Kaduna

Yan sandan Nigeria
'Yan Sandan Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: UGC

An kama shi ne a Ayama road, a garin Famgbe da ke ƙaramar hukumar Yenagoa na jihar Bayelsa.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata a Yenagoa ya ce yan sandan sun kwato bindigan pistol ta gargajiya, ƙunshin harsashi takwas, haramtattun kwayoyi, da sulken sojoji daga hannun wanda ake zargin.

KU KARANTA: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Butswat ya ce:

"Wanda ake zargin yana bawa rundunar yan sandan hadin kai kuma za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike."

Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Dakarun sojojin Nigeria na Sector 1 Operation Hadin Kai (OPHK) tare da taimakon Yan Sa-Kai na Civilian JTF, a ranar 3 ga watan Yuli sun kama wasu yan ta'addan kungiyar Boko Haram biyu, Premium Times ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa direktan sashin watsa labarai na rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce sojojin sun kama wasu kayayyaki da aka siyo domin kaiwa yan ta'addan.

Mr Nwachukwu ya ce sun kama gurneti na hannu, diga daya, mota daya, kekuna biyar, wayoyin salula biyu (Tecno da Infinix), man fetur da man juye.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel