Duk da ya taimaki Atiku a zaben 2019, Buba Galadima ya ce shi ba ‘Dan PDP ba ne

Duk da ya taimaki Atiku a zaben 2019, Buba Galadima ya ce shi ba ‘Dan PDP ba ne

- Injiniya Buba Galadima ya yi karin haske game da akidarsa a siyasa

- Buba Galadima ya bayyana cewa shi fa ba ‘dan jam’iyyar PDP ba ne

- Tsohon jigon na jam’iyyar CPC ya ce har gobe shi ya na tare da r-APC

Injiniya Buba Galadima, wanda tsohon-na-kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ya ce babu ruwansa da manyan jam’iyyu biyu da ke kasar nan.

Jaridar Premium Times ta ce ‘dan siyasar ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da Premium Times Centre for Investigative Journalism (PTCIJ) ta hada.

An yi wa wannan taro da aka yi a yanar gizo take da “Intra-Party Democracy in Nigeria: Challenges and Solution”, inda Injiniya Galadima ya yi jawabi.

KU KARANTA: Na ga cin kashi a lokacin da na ke aiki a Villa - Diyar Buba Galadima

Dattijon ‘dan siyasar ya gabatar da kansa a matsayin shugaban kungiyar rAPC da ta balle daga jam’iyyar APC, ya ce nan gaba za a ji duriyar tafiyar ta su.

“Ina so in yi babban gyara, ni ba ‘dan jam’iyyar PDP ba ne. Ba na cikinta. Ni shugaban ‘yan taware na rAPC ne, kuma har gobe a nan na ke.” Inji Buba Galadima.

Galadima ya ce: “Ina so ‘yan kasa su sani ba da dadewa ba, Najeriya za ta ji dawowar mu siyasa.”

Tsohon sakataren na jam’iyyar CPC wanda ta narke cikin APC, ya zama ‘dan taware kafin zaben 2019, ya kafa kungiyar rAPC da sunan za a kawo gyara a APC.

KU KARANTA: Shugabanni suna ta bata lokaci, an gagara samun tsaro - Sultan Sa’ad III

Duk da ya taimaki Atiku a zaben 2019, Buba Galadima ya ce shi ba ‘Dan PDP ba ne
Injiniya Buba Galadima Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Galadima wanda kafin 2018 ya na cikin kusoshin APC, ya zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da gaza cika alkuwaran da ta daukarwa al'umma a 2015.

Da yake bayani jiya, Buba Galadima ya ce shi da sauran ‘yan siyasa sun gaza daukar darasi a Najeriya.

Sauran wadanda suka gabatar da jawabi sun yarda cewa kudi ya na yaudarar al’umma wajen zabe, sannan kakaba ‘dan takara ya na jawo matsala a tafiyar siyasa.

Har ila yau, Buba Galadima ya na ganin idan ba a yi wa harkar zabe garambawul ba, siyasar Najeriya ba za ta taba cigaba ba, The Cable ta rahoto wannan labari.

Kwanaki tsohon Jigo na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya fito ya na zargin gwamnatin Najeriya da kokarin takawa ‘yan adawa burki.

Buba Galadima ya ce a dalilin a hana ‘yan adawa sukar shugaba Muhammadu Buhari ne ake yi wa masu fada-a-ji a kafafen yada labarai na zamani dauki dai-daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel