Wata Dattijuwa ta shiga littafin tarihi a Najeriya, ta kammala PhD bayan ta haura shekara 70
- Marinze Ifeyinwa Onyemachi Felicia ta kammala karatun Digirinta na PhD
- Wannan mata mai shekara 71 ta kafa sabon tarihi a Jami’ar Legas, UNILAG
- Jami’ar UNILAG ta ce wannan tsohuwa ta samu PhD a harshen Faransanci
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Marinze, Ifeyinwa Onyemachi Felicia, ta kafa sabon tarihi a jami’ar Legas wanda aka fi sani da UNILAG.
Felicia Ifeyinwa Marinze ta kafa tarihi a shekara 71
Marinze Ifeyinwa Onyemachi Felicia mai shekara 71 da haihuwa ta kammala karatun digirdigir, ta zama wanda ta fi kowa tsufa da ta samu digirin PhD.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto kwanaki, ba a nan kadai Felicia Ifeyinwa Marinze ta tsaya ba, tana cikin manyan dalibai mafi hazaka a bana.
KU KARANTA: An dauki sababbin Ma’aikata 2000 a hukumar FIRS - Kungiya
Shugaban jami’ar ta UNILAG, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, ya bayyana wannan a lokacin da aka yi bikin yaye daliban jami’ar, wanda shi ne karo na 51.
Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya ce Felicia Ifeyinwa Marinze mai lamba ta 849003042, ta karkare karatun digirinta na PhD a fannin harshen faransanci.
Tsangayar harsunan turai da nazarin karatun kasar waje ta amince da aikin wannan dattijuwa da ta yi bincike kan kwarewar masu karatun faransanci.
Taken aikin da Felicia Ifeyinwa Marinze ta yi shi ne: "Evaluation de la Competence Communicative Orale du Francais Des Apprenants Nationale Diploma Des Polytechniques Seledionness du Nigeria."
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace 'Yan makaranta a jihar Kaduna
Dalibi ya kammala B.Sc da 4.98
Farfesa Ogundipe ya ce Olatunji Moruf da Ekundayo Mesagan sune wadanda suka rubuta kundin PhD da ya fi kowane kyau a wannan shekarar a jami’ar.
Har ila yau shugaban jami’ar ya ce an yaye dalibai 15,753 a shekarar nan, daga cikinsu 281 sun kammala da matakin farko da ya fi kyau (First Class).
A cikin wadanda su ka yi digirinsu na farko, Alimi Ibrahim Adedeji ne ya ciri tuta, ya kare karatu da maki 4.98, sai Popoola Victoria Opeyemi mai 4.90 a biye.
A makon nan kun ji Farfesa Wole Soyinka ya na cewa garkuwa da Nnamdi Kanu aka yi, a cewar marubucin, ta haramtaciyyar hanya aka kama shugaban IPOB.
Farfesa Wole Soyinka ya na ganin ya ce ya kamata a ce an kama ‘Yan kungiyar Miyetti Allah kafin a jefa IPOB a cikin kungiyoyin da aka haramta aikinsu.
Asali: Legit.ng