Ba za mu iya fito da kai daga gidan yari ba, Matsayar Birtaniya kan tsare Nnamdi Kanu

Ba za mu iya fito da kai daga gidan yari ba, Matsayar Birtaniya kan tsare Nnamdi Kanu

  • Birtaniya ta bayyana cewa ba za ta iya fito dan kasarta daga gidan yari ba a wata kasa muddin an tsare shi kan saba dokar kasar ne
  • Kawai abin da za ta iya yi shine ta saka baki domin ganin an yi wa wanda aka tsare adalci wurin shari'a da bin dokokin kasar
  • Wannan matsayar na Birtaniya ya ci karo da kiran da dan uwan Nnamdi Kanu ya yi na cewa Birtaniya ta bukaci a sako shi saboda yana da izinin zama a kasar ta Birtaniya

Bisa ga dukkan alamu fatan da shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ke yi na cewa kasar Birtaniya za ta ceto shi daga gwamnatin Nigeria abu ne mai kaman wuya.

Kanu, wanda ke da shedan zaman dan kasar Birtaniya da kuma Nigeria yana tsare a hannun jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS a Abuja.

Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu, Shugaban kungiyar IPOB. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUAB WANNAN: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

An kama shi ne a kasar Kenya a ranar Asabar aka kuma taso keyarsa zuwa Nigeria a ranar Lahadi a cewar rahotanni daga bakin dan uwansa a wani rahoton Daily Trust.

Ana yi wa Kanu shari'a ne kan tuhumar cin amanar kasa da wasu laifukan amma aka bada belinsa bisa rashin lafiya a 2017 sai dai ya saba dokokin belin ya tsere daga kasar.

Daga inda ya ke a kasar waje, Kanu ya cigaba da ingiza mabiyansa suna ta kai wa hukumomin Nigeria hare-hare.

Da aka kai shi kotu a ranar Talata, Mai sharia Binta Nyako ta ce DSS su tsare shi har zuwa ranar 26 ga watan Yuli don cigaba da sharia.

Kanu da yan uwansa sun yi kira da hukumomin kasar Birtaniya su taimaka a sako shi domin ya koma gida wurin iyalinsa.

Sanarwar da dan uwan Nnamdi Kanu ya fitar.

Kingsley Kanu, dan uwan Nnamdi Kanu, cikin sanarwar da ya fitar ya ce:

"Ya kamata ofishin jakadancin Birtaniya a Nigeria ta matsa domin a saki dan uwa na nan take. Su tabbatar da tsaronsa. Ya zama dole Nnamdi Kanu ya koma Birtaniya wurin matarsa da dansa da ke zaune a can. Ya zama dole Sakataren kasashen waje na Birtaniya, Dominic Rabba, ta fayyace wa hukumomin Nigeria cewa ba za ta amince da tsare dan Birtaniya ba biza ka'ida ba kuma ta yi tir da abin da hukumomin Kenya da Nigeria suka yi."

Matsayar Birtaniya kan lamarin

Amma cikin wata takarda da Birtani ta wallafa a shafinta na intanet ta fayyace cewa abin da za ta iya game da yan Birtaniya da aka tsare a wasu kasashen na da iyaka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Mafarauta sun ɗirka wa mai garkuwa harsashi ya mutu yayin da yazo karɓar kuɗin fansa

Shafi na 19 na takardar ta ce:

"Muna iya baka bayanai cewa da tsarin fursuna na kasar, tare da tsarin zuwa ziyara, rubuta wasika, yiwuwar yin aiki da jin dadi da walwala da sauransu. Za mu iya maka bayanin banbance-banbancen da ke tsakanin wanda ake yanke wa hukunci da wanda ke zaman jiran shari'a.
"Ba za mu iya fitar da kai daga gidan yari ba ko inda ake tsare da kai, kuma ba zamu nemi a yi maka wata gata ba domin kai dan Birtaniya ne. Sai dai idan an saba dokoki yayin tsare ka muna iya tuntubar jami'an kasar. Hakan ya kunshi rashin yi maka adalci ko jinkirta yi maka shari'a fiye da kima akasin yadda ake yi wa sauran wadanda aka tsare."

Hakan na nufin kasar ta Birtaniya ba za ta iya tursasawa a saki duk wanda dokar kasa ke da hurumin tsarewa ba sai dai kawai ta bukaci a yi masa shari'a bisa tsarin dokar kasa da na kasashen duniya bisa adalci.

A wani labarin, kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi takatsantsan da lamarin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, rahoton Daily Sun.

A cewar kungiyar ta Arewa, shugaban na masu fafutikan kafa kasar Biafra yana da abokan hulda sosai a kasashen ketare.

Kungiyar ta yi wannan furucin ne yayin da ta ke martani kan sake kama shugaban na IPOB a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel