NCGP ta na so a hana duk ‘Dan siyasar da ya kai shekara 60 neman zama Shugaban kasa
- Kungiyar North Central Progressive Group ta tsoma baki a cikin siyasar 2023
- Shugabannin NCGP sun ce bai dace ‘Dan shekara 60 ya nemi shugaban kasa ba
- Kungiyar tana ganin lokaci ya yi da matashin Arewa ta tsakiya zai rike kasar
Kungiyar NCGP ta wasu mutanen Arewa maso tsakiya da ke son cigaba, ta ce wadanda su ka kai shekara 60 bai dace su fito neman kujerar shugaban kasa ba.
Wannan kungiya ta North Central Progressive Group wanda aka fi sani da NCGP ta ce ya kamata tsofaffin ‘yan siyasan yankin su hakura da batun zaben 2023.
NCGP ta ce za a haramta wa duk wani wanda ya kai shekaru 60 zuwa sama damar yin takara.
KU KARANTA: Zan yi takarar Shugaban kasa a 2023 - Yarima
Duk wanda ya kai shekara 60 ya hakura - NCGP
Daily Trust ta ce kungiyar ta NCGP ta yi wannan bayani ne lokacin da ta zanta da manema labarai a birnin tarayya Abuja, a ranar Talata, 6 ga watan Yuli, 2021.
A cewar kungiyar mafi yawan wadanda su ka rike mukaman siyasa a baya, matasa ne, don haka ta ke so a dawo da wannan al’ada na tafiya da masu jini a jika.
Shugabannin wannan tafiya; Benjamin Sani, Felix Tolorunju da Aisha Uju Okoye, sun yi wa ‘yan jarida jawabi, su ka ce akwai tulin matasan da za su iya mulki.
Kamar yadda Blueprint ta kawo rahoto, NCGP ta kuma bukaci duka jam’iyyun siyasan Najeriya su bar yankin Arewa ta tsakiya da Kudu maso gabas su yi mulki.
KU KARANTA: Gwamnonin Kudu sun sha banbam da Majalisa a kan PIB
Ya kamata a ba matasan mu dama su yi mulki
Benjamin Sani ya ce sun bijiro da wannan magana ne saboda ganin an maida matasa saniyar ware.
A cewar Sani, yankin Arewa maso tsakiya za su iya rike shugabancin kasar kamar yadda aka gani sa'ilin da Bukola Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa.
Shugaban na NCGP ya ce kujerar shugaban majalisar dattawa shi ne mafi girman mukamin da mutanen bangaren Arewa ta tsakiya suka rike a gwamnatin kasar.
“Mun shirya, mu na da irinsu tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, ga gwamnoni kamarsu gwamna Yahaya Bello na Kogi, da Bukola Saraki daga Kwara.”
A baya ku na da labarin Dattawan Arewa na kungiyar NEF sun soki kiran Gwamnonin Kudu na tsaida ‘Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 daga Kudancin kasar.
Kungiyar manyan Arewan ta maida wa Gwamnonin yankin raddi da cewa mutane ne su ke zabe.
Asali: Legit.ng