PIB: Kason da Jihohi za su tashi da shi wajen hako mai zai hada Gwamnoni fada da 'Yan Majalisa

PIB: Kason da Jihohi za su tashi da shi wajen hako mai zai hada Gwamnoni fada da 'Yan Majalisa

  • Kason da za a rika warewa jihohin Kudu idan an samu danyen mai ya jawo sabani
  • Gwamnonin kudancin Najeriya ba su gamsu da abin da Majalisa ta tanada masu ba
  • Kungiyar Gwamnonin sun kuma ki yarda da shawarar sauya tsarin mallakar NNPC

Gwamnonin yankin kudancin Najeriya sun ki karbar 30% da ake shawara a rika ba su daga cikin ribar da kamfanin NNPC ya samu wajen hako danyen mai.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa gwamnonin kudancin kasar ba su gamsu da matsayar da majalisar tarayya ta ci, na ware masu wannan kason ba.

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu SAN, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin yankin ya fitar da jawabi bayan zaman da aka yi.

KU KARANTA: Abin da ya sa wasu ‘Yan Kudu su ke kiran a tarwatse - Sanata

Gwamnonin kudu ba su amince da kudirin PIB ba

A taronsu na ranar Litinin, gwamnonin sun tattauna a kan wannan batu, inda su ka yabi ‘yan majalisa na amincewa da kudirin PIB da aka dade, ana ta jira.

“Kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya, a karshen taron da su ka yi a ranar 5 ga watan Yuli, 2021, sun duba batun halin tsaron da ake ciki a yau, yi wa dokokin kasa kwaskwarima, da dokar PIB ta harkar mai.”
“Kungiyar ba ta goyon bayan kashi 3% da majalisar wakilan tarayya ta ware domin a rika ba mutanen yannkin da aka samo danyen mai a cikin kasarsu.”
“Sannan kungiyar ba ta goyon bayan 30% da za a rika ba su daga ribar da aka samu wajen hako mai.”
Gwamnoni
Gwamnonin Kudu a wani taro Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Mu sa Fafaroma a cikin addu’o’inmu – Buhari

“Bayan haka kuma kungiyar ba ta goyi-bayan a dauke tsarin mallakar kamfanin NNPC ba.”
“Kungiyar ba ta goyon bayan kamfanin mai na kasa watau NNPC ya koma hannun ma’aikatar kudi ta tarayya, ya zauna a karkashin hukumar NSIA ta kasa.”

Dalilin haka shi ne jihohi da gwamnatin tarayya sun yi tarayya wajen mallakar NSIA a dokar kasa.

A baya kun ji sauyin da sabuwar dokar PIB da aka yi shekaru 20 ana jira za ta kawo sun hada da kashe aikin hukumomin PEF da PPPRA bayan an amince da kudirin.

Idan an amince da kudirin PIB, NNPC zai koma hannun Minista a karkashin ma’aikatar kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel