Muna kashe N60b a kowace shekara domin gyaran bututun man da aka lalata
- Gwamnatin Tarayya ta koka da aika-aikar da masu lalata bututan man da sauran harkokin gas suke haifar wa ga tattalin arzikin kasar
- Ministan Yada Labarai ya ce gwamnatin na asarar kimanin naira biliyan 60 a duk shekara wajen kula da bututan man
- A cewarsa, kusan kashi 80 na kasafin kudin Najeriya yana samuwa daga sayar da man
Gwamnatin Tarayya ta ce tana kashe kudi har N60b a kowace shekara domin gyara da kuma kula da bututun mai da aka lalata a fadin kasar.
Ta kuma ce kasar na hasarar akalla ganga 200,000 a kowace rana sakamakon aika-aikar lalata bututun mai da sauran kayayyakin mai da iskar gas.
Ministan Yada Labarai da Raya Al'adu, Alhaji Lai Mohammed shi ne ya bayyana hakan a taron wani taro kan kare albarkatun mai da iskar gas da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, rahoton Vanguard.
Ya bayyana cewa taron nada matukar muhimmanci, duba da cewa lalata kayayyakin yana da tasirin gaske ga tattalin arziki da muhalli ga gwamnati da al'ummomin da ake hakar albarkatun a cikinsu, idan aka yi la’akari da cewar mai yana samar da kashi 80 na kudaden shigar Najeriya da kuma kashi 95 na kudaden wajen da kasar ke samu a hada-hadar kudaden shigar da take samu daga ketare.
DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya
KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari
Yace:
“Lura da mai yana samar da mai da kashi 80 kasafin kudin Najeriya da kashi 95 na kudaden shigar kasashen waje, ana iya fahimtar illar tasirin da fasa bututan mai ke haifar wa ga tattalin arzikin.
‘‘Tsakanin watan Janairun 2019 da Satumban 2020, an lalata bututun mai sau 1,161 a duk fadin kasar nan.
“Baya ga tasiri kan kudaden shigar da kasar ke samu, ku kuma yi la’akari da matsalolin muhalli da barna mai dorewa da abin ke haifarwa kan gurbata ruwa da gurbatar iska da gurbatar kasar wurin da sauransu, kuma za ku fahimci girman matsalar.
Haka nan taron yana da zimmar wayar da kan 'yan kasa wajen dafawa gangamin kan bada kariya da sanin muhimmancin mallakar ababen more rayuwa na gwamnati musamman a bangarorin layukan dogo da tituna da kuma sufurin jiragen sama.
Yayin da yake jaddada bukatar kare ababen more rayuwar jama'a, Ministan ya kara da cewa wannan gwamnatin ta fara zuba jari mai yawa a bangaren tun lokacin da ta hau karagar mulki, duk da raguwar kudaden shigar da take samu, riwayar Punch.
Mun yi asarar N51.207b, NNPC
A cikin bayanin da ya gabatar, Manajan Daraktan Kamfanin Mai na NNPC, Mele Kyari ya ce Kamfanin ya yi asarar kimanin N51.207b tsakanin shekarar 2019 zuwa Mayun 2021.
Daga Janairu zuwa Disamban 2020, ya ce kamfanin ya yi asarar da taki litar mai miliyan 146.809 da darajarsa ta kai N22.487b.
Ya bayyana wuraren da suka fi kaurin suna a fagen lalata bututan man da cewa a yankunan Abagbo da Ikate da Akaraba da Ilashe da Imoren da Ijegun da Ikotun da Baruwa da Oke Odo da Warewa da kuma Ilara.
Naira N256 ya kamata a rika sayar da litan man fetur
Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya ce farashin litan man fetur zai cigaba da kasancewa N162 a watan Yulin da za'a shiga kuma ba za'a kara ba.
Shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunruse Daily na tashar Channels ranar Talata.
Ya ce ana cigaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago kan farashin da ya kamata a sanya.
Asali: Legit.ng