Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

  • Shugaba Buhari ya jaddada imaninsa da aikin noma
  • Buhari a labaran da ya samu, mutane a koma gona kuma ba suyi nadaman haka ba
  • Ya karbi bakuncin tsohon Firai Ministan kasar Ethiopia

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tsarin noman da gwamnatinsa ta kirkiro na haifar 'da mai ido saboda mutane sun fara ajiye ayyukansu na ofis suna komawa gona.

Buhari ya ce man fetur ba zai iya ciyar Najeriya ba yanzu.

Yayin magana a fadar Aso Villa ranar Juma'a yayin karban bakuncin tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Dessalegn, Buhari ya ce gwamnatinsa ya mayar da hankali kan aikin noma kuma ta rage dogaro da man fetur.

A jawabin da mai magana da yawunsa ya saki, Shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta dakatad da shigo da kayan abinci daga kasashen waje, kuma saboda hakan yan Najeriya ke shuka abinda suke ci yanzu.

Mutane na ajiye ayyukansu a Ofis suna komawa gona: Buhari
Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yace:

"Akwai bukatar mu koma gona, saboda man fetur ba za iya ciyar da kasar ba yanzu, musamman rashin tabbas na farashinta."
"A yau abinda muka shuka muke ci, kuma mun hana shigo kayan abinci da yawa."
"Noma ya taimaka mana wajen samar da ayyukan yi. Kuma wasu mutane na ajiye ayyukansu na ofis don komawa gona. Labarin da muke samu kenan.

A nasa bangare, tsohon Firai Ministan ya jinjinawa shugaba Buhari bisa nasarorin da ya samu musamman wajen dakile cutar COVID-19 da aikin noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng