Da duminsa: Duk da cewa N256 ya kamata, ba zamu kara farashin man fetur ba a watan Yuli, NNPC

Da duminsa: Duk da cewa N256 ya kamata, ba zamu kara farashin man fetur ba a watan Yuli, NNPC

  • Babu karin farashin litan mai a watan Yuli
  • NNPC ya cigaba da salon sanar da hakan kowani wata don hana yan kasuwa haifar da wahalan mai
  • Gwamnati ta ce dole yasa ta cigaba da biyan kudin tallafin mai

Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ya ce farashin litan man fetur zai cigaba da kasancewa N162 a watan Yulin da za'a shiga kuma ba za'a kara ba.

Shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunruse Daily na tashar Channels ranar Talata.

Ya ce ana cigaba da tattaunawa da kungiyoyin kwadago kan farashin da ya kamata a sanya.

Kawo yau Talata, 29 ga Yuni, farashin danyen mai ya tashi zuwa $74.72 ga ganga a kasuwar duniya

Mele Kyari ya ce duk da haka ba za'a kara farashin litan man fetur ba har sai an gama tattaunawa da yan kwadago.

Yace duk da cewa N256 ya kamata a rika siyar da litan mai saboda farashin danyen mai a kasuwar duniya, NNPC ba zata kara daga N162 ba.

Yace shugaba Buhari ya umurci NNPC yayi dukkan mai yiwuwa don saukakawa yan Najeriya sayan man fetur, musamman a wannan lokaci.

Yace:

"Abinda hakan ke nufi shine muna daukan kudi da ake amfani da shi wajen biyan rarar."

KU KARANTA: Wata mata tana neman mutumin da ta aura a dandalin taron dalibai tun lokacin suna firamare

Kamfanin NNPC
Kamfanin NNPC Hoto: NNPC
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

NNPC za ta ci bashi domin samun kashi 20 a matatar man Dangote

A kan maganar matatar man Dangote kuwa, shugaban NNPC yace gwamnatin Najeriya za ta saya hannun jarin kashi 20% na matatar don tabbatar da tsaro.

Ana sa ran matatar za ta fara aikin tace man a shekarar 2022 inda za tana tace ganga 650,000 a kowace rana.

"Babu yadda zai yiwu mu bari babban kasuwa irin wannan a bar mutum guda yana yadda yaso," yace.

Ana ganin matatar a matsayin gagaruma ta fuskar inganta makamashi a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel