COAS Yahaya ya gwangwaje tsohon jarumin fim Samanja da kyautar N2m

COAS Yahaya ya gwangwaje tsohon jarumin fim Samanja da kyautar N2m

  • Manjo Janar Farouk Yahaya, shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya ya gwangwaje tsohon jarumi Samanja da kyautar N2m
  • Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama a fina-finai, ya musanta rade-radin mutuwarsa da ake yadawa
  • COAS yace Samanja ya kasance mai kishin kasa kuma mai wayar wa jama'a kai a fannin rayuwar soja da ta bariki

Kaduna

Shugaban rundunar sojin kasa, COAS Manjo Janar Faruk Yahaya a ranar Litinin ya gwangwaje tsohon jarumin fina-finai, Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama da kyautar naira miliyan biyu a Kaduna.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa COAS ya bada wannan kyautar ne bayan ya ziyarci tsohon jarumin a gidansa.

NAN ta ruwaito yadda jarumin ya karyata rade-radin dake yawo na cewa ya mutu a kafafen sada zumunta a kwanakin da suka gabata.

KU KARANTA: Iyaye sun fusata kan dalilin El-Rufai na cire dan shi daga makarantar gwamnati

COAS Yahaya ya gwangwaje tsohon jarumin fim Samanja da kyautar N2m
COAS Yahaya ya gwangwaje tsohon jarumin fim Samanja da kyautar N2m. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

COAS ya samu wakilcin Birgediya Janar Vitalis Okoro, babban kwamandan GOC 1 Div na rundunar soja a Kaduna.

COAS ya jinjinawa tsohon jarumin

Yahaya yayi bayanin cewa an sanar da shi rashin lafiyan tsohon jarumin kuma ya ji ya zama dole ya bada tashi gudumawar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce rundunar sojin Najeriya tana alfahari da irin mutanen da suka bada gudumawarsu a al'umma.

Kamar yadda yace, rundunar sojin tayi matukar farin ciki kan yadda Samanja ya dinga daga darajar rundunar a idon 'yan Najeriya tare da nuna musu yadda rayuwa a bariki take.

"Da wannan muhimmin rawa da ya taka, ya samarwa kansa wuri a masana'antar nishadi. Baya ga haka, ya kasance abun duba idan aka kira sunan rundunar sojin Najeriya," yace.

Samanja ya yi godiya

A yayin martani, Samanja cike da farin ciki ya mika godiyarsa da COAS da ya tuna da shi. Yayi kira ga sauran 'yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa tare da addu'ar zaman lafiya a Najeriya.

Ya yi kira ga matasa da su kasance masu ayyukan da zasu amfanesu a rayuwa, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a Zangon kataf ta Kaduna

A wani labari na daban, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce ba zai yi murabus daga siyasa ba har sai ya mutu, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai bayan rantsar da majalisar Shura ta jihar Kano, Shekarau ya ce "ba ni da lokacin yin murabus daga siyasa har sai na mutu."

Tsohon gwamnan har sau biyu na jihar Kano, ya samu mukamin ministan ilimi daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma yayi fafutuka a zaben 2015 ba kadan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel