Sanatan Arewa ya tona abin da ya sa wasu ‘Yan Kudu su ke ta fafutukar a wargaza Najeriya

Sanatan Arewa ya tona abin da ya sa wasu ‘Yan Kudu su ke ta fafutukar a wargaza Najeriya

  • Sanata Abdullahi Adamu ya ce harin 2023 ya sa ake kiran Najeriya ta wargaje
  • Tsohon Gwamnan ya na ganin neman kujerar Shugaban kasa ya sa ake surutai
  • ‘Dan siyasar ya ce zargin an maida wani yankin saniyar ware ba gaskiya ba ne

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu, ya yi hira da Daily Trust TV, inda ya yi magana a kan batutuwan da su ka shafi cigaban kasa da gwamnati.

Sanata Abdullahi Adamu wanda shi ne shugaban kwamitin harkar gona da cigaban karkara a majalisar dattawa, ya fadi abin da jawo ake kiran a wargaza Najeriya.

Kujerar shugaban kasa ake kwadayi ba komai ba - Adamu

“Na yi imani cewa ana fama da rashin tsaro da kururuwan a raba kasa daga wajen shugabannin Kudu saboda suna ganin ba su cin wata ribar gwamnati.”

KU KARANTA: Doka ta bukaci Buhari ya yi maganin Kanu - Lauya

“Wani lokaci sai ka rika mamakin ko korafin me su ke yi. Idan ka duba duk wasu manyan kujeru a kasar nan, za ka samu Ibo, Bayarabe da mutanen Neja-Delta.”
“Wannan surutun duk saboda neman shugaban kasa ne.”
“Matsalarsu ita ce a kan menene Bahaushe zai hau kujerar shugaban kasa bayan Buhari? Ba na yin wani kame-kame; na tsufa, na kuma san yadda Najeriya ta ke aiki.”

Gwamnatin Buhari ta na tafiya da kowa

Da ‘yan jarida su ka tambayi Abdullahi Adamu a game da zama da masu wadannan kira na a raba Najeriya, sai ya ce sai an yi hattara ka da a fada tarkon masu mugun nufi.

KU KARANTA: Bai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba - El-Rufai

Sanata Abdullahi Adamu
Sanata Abdullahi Adamu Hoto; www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Sanatan ya ce mutanen sauran bangarorin kasar nan suna samun mukamai masu tsoka. A ra’ayinsa, idan aka tattara mukaman, za a ga 'Yan Arewa ba su da yawa.

Jami'an Arewa su ke rike duk wasu manyan mukamai
"Wace kujera ce mai tsoka, kowane bangare na gwamnati ya na da muhimmanci a wuri na. Wanene gwaman CBN? Ministan ayyuka? Ministan kiwon lafiya?"
“Menene ake kira ba-ba-ke-re? Sha’anin tsaro yana da tsari, ba za ka dauka wanda bai yi nisa ba, ka bashi mukami, z aka jagwalgwala lamarin. Shuru kurum ake yi”

A makon nan ne ake jin cewa kungiyar Movement for the Actualization of the Sovereign State of Biafra watau MASSOB ta gama shirin zuwa kotu da shugaban Najeriya.

Wannan kungiya mai rajin kafa kasar Biyafara mai ‘yancin kanta a Najeriya ta na kokarin zuwa kotu da Muhammadu Buhari a dalilin Nnamdi Kanu da Sunday Ogboho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel