2023: ‘Yan siyasan Arewa 7 da Gwamnonin Kudu su ke shirin yi wa bukulun shiga Aso Villa

2023: ‘Yan siyasan Arewa 7 da Gwamnonin Kudu su ke shirin yi wa bukulun shiga Aso Villa

  • Gwamnonin Kudu sun ce dole daga yankinsu za a samu Shugaban kasa mai zuwa
  • Hakan zai zama cikas ga ‘Yan siyasan Arewa da su ke sha’awar wannan kujerar
  • Daga cikin wadanda ake tunani za a tauye akwai jagoran adawa, Atiku Abubakar

A ranar Litinin ne kan Gwamnonin jihohin kudancin Najeriya 17, ya hadu a kan cewa dole shugaban kasan da za ayi na gaba ya fito daga yankinsu.

Kungiyar SGF ta gwamnonin kudu sun yi taro a Legas, inda suka dauki matakin da ake ganin zai iya jawo wa wasu ‘yan siyasan yankin Arewa cikas a 2023.

Daily Trust ta ce akwai ‘yan siyasan Arewa da ake kyautata zaton su na harin kujerar shugaban kasa, daga cikinsu har da tsohon mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA: 2023: Wadanda su ka halarci UNIJOS su na goyon bayan Yahaya Bello

Jerin ‘yan siyasan da su ke sha'awar takarar Shugaban kasa

1. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

2. Tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

3. Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal

4. Gwamnan Kogi, Yahaya Bello

5. Tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yarima

6. Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed

7. Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

A cikin wannan jeri, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da kuma jigon APC a jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ne kurum ‘Yan APC.

Bayan Bala Mohammed, duk ragowar sun bi jam'iyyar APC kafin su dawo PDP mai adawa.

KU KARANTA: Gwamnoni da ke kwadayin kujerar shugaban kasa a zaben 2023

Jam'iyyar PDP a Legas
PDP ta na yakin neman zabe a 2019 Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Daga kudancin Najeriya, wadanda ake kyautata suna harin kujerar shugaban kasa sun hada da Asiwaju Bola Tinubu, Dr. Kayode Fayemi da Dave Umahi.

Sai kuma Sanata Rochas Okorocha, Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi da Donald Duke.

Gwamnonin da su ka dauki wannan matsaya

Kun san Gwamnonin da su ka halarci taron jiya su ne: Rotimi Akeredolu; Dapo Abiodun, Gboyega Oyetola, Ifeanyi Okowa, Nyesom Wike da Seyi Makinde.

Ragowar sun hada da Kayode Fayemi, Douye Diri, Ifeanyi Ugwuanyi da Emmanuel Udom.

Gwamnonin Anambra da Kuros Riba ba su samu zuwa ba, sai Godwin Obaseki, Hope Uzodinma, Dave Umahi, da Okezie Ikpeazu su ka turo mataimakansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng