Da dumi: ’Yan Majalisar Wakilai guda hudu sun fice daga PDP zuwa APC
- Zuwa yanzu ’Yan Majalisar Tarayya shida ne suka bi sahun Gwamna Matawalle zuwa Jam’iyyar APC
- ’Yan Majalisar sun ce rikicin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PDP shi ne silar ficewarsu daga jam’iyyar
- Sun sanar da sauya shekar a zaman Majalisar na ranar Talata
Wadansu Mambobin Majalisar Wakilai guda hudu da aka zaba karkashin inuwar Jam’iyyar PDP daga Jihar Zamfara a ranar Talata sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC.
Sun ba da hujjar sauya shekar da suka yi da rikicin cikin gida da suka ce jam'iyyar PDP na fama da shi.
’Yan Majalisar sune Bello Hassan Shinkafi da Ahmed Bakura da Ahmed Shehu da Suleiman Gumi.
A wata wasika da Dan Majalisa Suleiman Gumi ya sanyawa hannu kuma aka karanta a zaman majalisar na ranar Talata, ’yan majalisar sun ce sun fice daga Jam’iyyar PDP ne saboda rikicin da ke cikin jam’iyyar, wanda ya haifar da rusa shugabancin jam’iyyar a jihar da shugabannin jam’iyyar na kasa suka yi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ’Yan Majalisar PDP shida daga jihar sun amince tafiya tare da Gwamna Bello Matawalle na jihar zuwa APC
DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya
KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari
Dan majalisa daya tilo da yaki fita daga PDP a Zamfara
Honarabul Salihu Usman Zurmi wanda ake kira Gurgu, shi kadai ne ya rage a cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar dokokin jihar Zamfara.
BBC Hausa ta yi hira da Salihu Usman Zurmi, domin jin abin da ya sa ya ki shiga jirgin APC.
Ganin irin alherin da PDP ta yi masa, ta ba shi tikitin shiga takara, don haka Salihu Usman Zurmi mai wakiltar mazabar Zurmi ta gabas, ya ki bin APC.
Asali: Legit.ng