Yarbawa Sun Nuna Su 'Yan Amana Ne, In Ji Tsohon Kakakin APC, Timi Frank

Yarbawa Sun Nuna Su 'Yan Amana Ne, In Ji Tsohon Kakakin APC, Timi Frank

  • Tsohon kakakin jam'iyyar APC na kasaTimi Frank ya yabawa Yarabawa akan abun da ya kira nuna kishin kasa
  • Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APCn ya ce kusan dukkanin manyan yarabawa da jagororinsu suna tare da al'ummarsu
  • Frank ya ce Sunday Igboho jagora ne na gari da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda ceto al'ummarsa

Tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC na kasa kuma dan gwagwarmaya haifaffen jihar Bayelsa, Timi Frank, ya ce Yarabawa sun nuna cewa za a iya amince musu, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce Yarabawan sun nuna amana a abin da ya kira 'nasarar gangamin kasar Yarabawa na 3 ga Yuli 2021' da aka gudanar a Legas, Nigeria.

Tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na APC, Timi Frank
Timi Frank, tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na APC. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kungiyoyin CAN da HURIWA sun buƙaci El-Rufai ya yi murabus bayan garkuwa da ɗalibai 26 a Kaduna

A wata tattaunawa da yayi da wani dan jarida, Susan West, dan gwagwarmayar ya ce, "toh da farko dai zan fara yabawa Yarabawa kan abin da suka yi yau. Sun nuna su yan kishin kasa ne, sun nuna cewa za a iya dogaro da su. Sun nuna za a iya yadda da su".
"Duk da tsoratarwa daga wajen gwamnati, duk da haka sun gudanar da abin su. Da iya wannan, na yaba musu kuma ina tunanin Sunday Igboho ya nuna cewa mutum ne mai magana daya."

Ya nunawa duniya cewa shi jagora ne na kwarai, jagora da ya yarda da mabiyansa kuma zai iya mutuwa saboda su.

KU KARANTA: El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba

To a tunanina, yau al'ummar Yarabawa, ko muna so ko bama so, sun nuna cewa manyansu da jagororinsu, da yawan su suna tare da mutanensu," kamar yadda ya bayyana.
Ya ce Tinubu, dole ya goyi bayan mutanensa. Ya ce, "yanzu lokaci ne da ya kamata yan kasar Oduduwa su ji matsayarsa, kasar Oduduwa ko kuma ba nan ba."

Rahoton na Vanguard ya kuma ce tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC ya ce Yarabawa su girmama Sunday Igboho wanda ya tsaya musu kai da fata.

Ya ce ya kamata Buhari ya duba yiwuwar ko kasar Oduduwa za ta samu hanyar da za a fitar da ita. Ya fadi abu iri daya ga kudu maso gabas.

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan sandan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel