Ka cancanta: Tsofaffin Dalibai suna goyon bayan gwamnan APC ya nemi takarar Shugaban kasa

Ka cancanta: Tsofaffin Dalibai suna goyon bayan gwamnan APC ya nemi takarar Shugaban kasa

  • Kungiyar tsofaffin daliban jami’ar UNIJOS ta karrama Gwamna Yahaya Bello
  • Shugaban kungiyar na kasa, Nuhu Johnson, ya ba gwamnan Kogi lambar yabo
  • SSG Folashade Ayoade ta halarci bikin da aka shirya, ta wakilci Gwamna Bello

The Cable ta ce a karshen makon da ya gabata tsofaffin daliban jami’ar tarayya da ke garin Jos, jihar Filato (UNIJOS), ta yabi aikin gwamnan Kogi.

Shugaban kungiyar tsofaffin daliban na jami’ar UNIJOS, Mista Nuhu Johnson, ya nuna cewa su na tare da Yahaya Bello idan har zai yi takara a 2023.

Nuhu Johnson wanda shi ne shugaban kungiyar wadanda su ka halarci wannan jami’a a fadin Najeriya, ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta wuce.

KU KARANTA: Taurarin Super Eagles su na goyon bayan Yahaya Bello a 2023

Kungiya ta karrama Yahaya Bello da Muhammed Onogwu

Kungiyar ta shirya wani biki domin ta karrama daya daga cikin ‘ya ‘yanta, Muhammed Onogwu, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kogi.

Johnson ya bayyana Mai girma gwamna Yahaya Bello a matsayin ‘guguwar canji’, ya ce gwamnan ya yi kaurin suna wajen bauta da hidimar jama'a.

Shugaban kungiyar tsofaffin daliban da su ka halarci UNIJOS ya yabi gwamnan, saboda kokarin da yake yi wajen kawo wa Kogi abubuwa na more rayuwa.

Har ila yau Johnson ya bayyana cewa Bello ya canza rayuwar mutanen da ke Kogi da wajen jihar. Jaridar nan ta Blueprint ta tabbatar mana da wannan rahoto.

Gwamna Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Fastocin neman takarar Yahaya Bello suna yawo a garin Abuja

Gwamna Yahaya Bello ya fita zakka

“A matsayinsa na ‘dan kishin-kasa, gwamna Yahaya Bello, yahau kujerar gaba wajen kawo hadin-kai, da tabbatar da cewa Najeriya ba ta wargaje ba.”
“Saboda mutum ne shi na kwarai, mai gaskiya, abin dogara, ya tsoma bakinnsa a rikice-rikicen da ake yi, wadanda za su iya jefa kasar a cikin yamutsi.”

Sakatariyar gwamnatin Kogi, Folashade Ayoade, ta wakilci gwamnan a wajen wannan biki, ta kuma karbi kyautar da aka ba shi, ta jinjina wa wannan kungiya.

Ku na sane cewa Gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya na cikin wadanda su ke sa ran fito wa neman takarar zama shugaban kasa a APC a zabe mai zuwa na 2023.

Bello da bakinsa ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya tsaya takara, saboda mutane na rokonsa ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng