Abubuwa 6 da ya dace kowa ya sani kan 'PIB' da za ta sa a saida NNPC, a kashe PEF da PPPRA
Majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da kudirin PIB cikin makon nan. Idan wannan kudiri ya zama doka, zai kawo gyara a tsarin tattalin arzikin Najeriya.
Wannan kudirin zai canza yadda kamfanin NNPC yake aiki tare da tabbatar da yin gaskiya. Mutanen yankin da ake hako mansu za su amfana da kudirin.
Legit.ng Hausa ra kawo wasu daga cikin hanyoyin da wannan kudiri zai canza harkar mai a kasar.
Saida kamfanin NNPC
PIB zai bada damar a saida kamfanin mai na kasa watau NNPC. Sannan za a saida hannun jarin gwamnati da ke kamfanin, a damkawa hannun Ministar kudi.
Kamfanin NNPC zai koma NNPC Limited a karkashin kulawar ‘yan kasuwa, idan PIB ta samu karbuwa. Jaridar Daily Trust ce ta tabbatar da wannan rahoto.
KU KARANTA: Majalisa ta amince da dokar PIB da aka dauki shekaru ana dogon turanci
Soke Hukumomin Gwamnati
Idan wannan kudiri ya samu shiga, za a kashe hukumomin Petroleum Equalisation Fund (PEF) da Petroleum Products Pricing Regulatory Agency (PPPRA).
Wadannan hukumomi ne suke da alhakin tsaida farashin kayan mai da tabbatar da an saida man a kan wadannan farashi da hukumar gwamnati ta kayyade.
3% na ribar da aka samu zai tafi wajen gina al’ammu
Kashi 30% na ribar da kamfanin NNPC ya samu wajen aikin hako gas da mai zai tafi wajen kawo cigaba ga yankin da ake hako danyen man daga cikin kasarsu.
Bayan haka za a rika karbar 3% na kudin da kamfanonin mai su ke batar wa a kan wannan aikin. Wannan kudi sun haura Dala miliyan $500 a kowace shekara.
Gwamnati za ta lafta wa kamfanonin mai harajin HT da CIT
African Business ta ce kamfanonin da su ke aiki za su rika biyan haraji duk shekara. Za a karbi harajin HT da na CIT gwargwadon lasisin da aka ba kamfani.
KU KARANTA: PIB: Sabuwar dokar mai za ta ruguza aikin NNPC da PPPRA
Za a kara kaimi wajen cin tarar masu saba doka
Tarar da za a rika cin kamfani bayan shigo da kudirin PIB ya karu; daga N10, 000, wadanda su ka saba doka a karon farko za su rika kashin N100, 000, 000 a yanzu.
Sababbin hukumomin gwamnati su na hanya
Wani sashe na kudirin ya bada damar kafa Nigerian Upstream Regulatory Commission da kuma Nigerian Midstream & Downstream Petroleum Regulatory Authority.
A makon nan ne Mele Kyari ya bayyana cewa NNPC za ta dauki watanni 18 kafin ta gama gyara matatun danyen mai Warri da na Kaduna da ake shirin gyara wa.
Shugaban na NNPC ya kuma bayyana cewa saboda biyan tallafin fetur da ake yi, fiye da 60% na kudin da NNPC ta ke zuba wa a cikin asusun FAAC ya ragu a bana.
Asali: Legit.ng