Buhari ya yi wa Fafaroma baran addu’o’i yayin da za a shiga da shi tiyata a asibiti
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a taya Fafaroma da addu’o’i a ko ta ina
- Za a yi wa Shugaban mabiya darikar Katolika da ke fadin Duniya aiki a asibiti
- Buhari ya roki Ubangiji ya sa ayi wannan aiki lafiya, a fito da Fafaroman lafiya
Shugaba Muhammadu Buhari ya fito, ya yi magana yayin da ake shirin shiga da fafaroma asibiti, inda za ayi masa wani aiki a tumbinsa.
Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban Najeriyar ya fitar da jawabi na musamman ne ta bakin hadiminsa, Malam Garba Shehu.
A jawabin fatan alheri da Allah ya ba ka lafiya da shugaban Najeriyar ya yi, ya roki Ubangiji ya yi gaggawar ba Fafaroma lafiya bayan aikin.
KU KARANTA: COVID-19 ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis
Garba Shehu, wanda ke taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari wajen yada labarai ya fitar da jawabin ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuli.
Jawabin shugaban Najeriya
“Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon samun lafiya ga shugaban cocin darikar katolika, Fafaroma Francis, yayin da ake shirin yi masa aiki a hanji.”
“Shugaban kasar ya kuma yi kira ga mutanen Najeriya da sauran kasashen Duniya su sa Fafaroma a addu’a, a daidai lokacin da za ayi masa wannan aiki.”
“Ya na yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.”
KU KARANTA: MASSOB na lallabar Amurka da Majalisar Dinkin Duniya su agazawa Biyafara
An yi wa Fafaroma aiki lafiya kalau
Rahotanni daga Reuters sun ce har an ayi wa Fafaroma Francis aiki a uwar hanjinsa. Babban hadiminsa ya ce ya fara samun sauki a gadon asibiti.
Wannan ne karon farko da Fafaroman mai shekara 84 ya kwanta, aka yi masa aiki tun da ya zama jagoran kiristocin da ke bin darikar katolika a 2013.
Mai magana da yawun Fafaroman, Matteo Bruni, ya ce ya soma murmure wa bayan an fito da shi, an ce sai da aka yi masa allurar barci kafin a barka shi.
Idan za ku tuna, kwanaki sai da Fafaroma Francis ya fito ya soki harin da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai a garin Zabarmari, da ke jihar Borno.
Babban limamin na kasar Rome ya soki harin ta’addan a hudubar da ya saba yi a kowane mako. 'Yan Boko Haram sun hallaka mutane da-dama a lokacin.
Asali: Legit.ng