NCSU: Ana kukan babu wuraren aiki, FIRS ta lallaba ta dauki Ma’aikata fiye da 2, 000 a boye

NCSU: Ana kukan babu wuraren aiki, FIRS ta lallaba ta dauki Ma’aikata fiye da 2, 000 a boye

  • NCSU ta ce an dauki ma’aikata sama da 2000 a boye a hukumar FIRS
  • Kungiyar ma’aikatan ta ce an yi wannan ne a watanni 18 da suka wuce
  • Ana zargin wannan ya jawo biyan albashin ma’aikata ya na yin wahala

Kungiyar ma’aikatan gwamnatin tarayya watau NCSU ta ce daukar ma’aikata da aka yi a boye, ya sa hukumar FIRS ta na fuskantar matsin lambar kudi.

Albashi sai an yi da gaske a FIRS

Punch ta fitar da rahoto a ranar Talata, 6 ga watan Yuli, 2021, cewa biyan albashi na neman ya gagari hukumar tun da aka dauki sabbabbin ma’aikata.

Sababbin ma’aikata fiye da 2, 000 aka dauka a hukumar FIRS mai tattara wa Najeriya kudin-shiga, a lokacin da ake ta kukan babu wuraren aiki a gwamnati.

KU KARANTA: Tsofaffin Daliban UNIJOS su na goyon Yahaya Bello ya zama Shugaban kasa

Wannan kungiya ta aika takarda zuwa ga shugaban FIRS na kasa, Nuhammad Nami a ranar 21 ga watan Yuni, ta na rokon ya sallami wasu rukunin ma’aikata.

Akwai darektoci da wasu jami’ai da FIRS ta dauka aiki, wanda ake kara masu wa’adi wata-wata.

Jaridar ta ce a wannan wasika da Idris Abdulrahman ya sawa hannu, an ba shugaban FIRS, Nami, wa’adin kwanaki 21 domin ya kori wadannan ma’aikatan.

Kungiyar ta fadakar da Ministar tattalin arziki, kungiyar kwadago, majalisar zartarwa, kungiyar ma’aikatan gwamnati, da ma’aikatar FIRS a kan batun.shi.

Shugaban FIRS
Muhammad Mamman Nami Hoto: independent.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Zarar $25m daga CBN ya sa an kai Gwamnatin Najeriya kotu

Kungiyar ta fadakar da Ministar tattalin arziki, kungiyar kwadago, majalisar zartarwa, kungiyar ma’aikatan gwamnati, da ma’aikatar FIRS a kan wannan batu.

NCSU ta kuma bukaci a biya ma’aikata alawus din aikin da su ka yi a shekarar da ta gabata.

Amma hukumar ta karyata zargin, ta ce biyan albashi bai yi mata wahala. FIRS ta musanya zargin ne ta bakin mai magana da yawunta, Abdullahi Sumaila.

A farkon shekarar nan ne fadar shugaban kasa ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya raba ayyuka ga wasu matasa 110 da suka yi wa kasa bauta a 2018.

Daga baya an ji shugaba Muhammadu Buhari ya na gargadi ga matasan da su ka yi Digiri cewa duk guraben ayyukan da ake da su a gwamnati, sun cika makil.

Asali: Legit.ng

Online view pixel