SERAP ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu a kan zarar Naira Tiriliyan 9.7 daga bankin CBN

SERAP ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu a kan zarar Naira Tiriliyan 9.7 daga bankin CBN

  • SERAP ta na karar Gwamnatin Najeriya a kotun tarayya da ke Abuja
  • Kungiyar ta na neman bayani a kan duk kudin da ake zara daga CBN
  • Kolawole Oluwadare da Adelanke Aremo suka shigar da wannan kara

An kai karar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wani babban kotun tarayya da ke garin Abuja, a dalilin kudin da gwamnatinsa ke karba daga CBN.

Jaridar PM News ta ce kungiyar SERAP ta bukaci gwamnatin tarayya ta yi bayani kan dala miliyan 25 da aka cire daga asusun babban bankin Najeriya.

SERAP ta na so a rika yin ke-ke-da-ke-ke

Wannan kungiya mai rajin kare hakkin al’umma da tabbatar da gaskiya ta na so ayi wa kowa karin haske a kan abin da ake yi da kudin da aka cira daga CBN.

KU KARANTA: MASSOB ta za ta kai Gwamnatin Tarayya zuwa kotun ICC

Rahoton ya ce kungiyar ta SERAP ta na so Alkali ya tursasa wa gwamnatin tarayya ta fadi ayyukan da tayi da abin da ta karba daga babban bankin tun 2015.

Haka zalika kungiyar ta na so shugaban kasa ya yi bayanin ko wannan kudi har dala miliyan 25 (Naira Tiriliyan 9.7) bai haura 5% na kudin shigar gwamnati ba.

Kungiyar SERAP ta yi amfani da damar da dokar FoI ta bada, ta shigar da wannan kara a kotu.

“A fito da bayanin kudin da aka zara da abin da aka biya, domin mutanen Najeriya su tabbatar da cewa gwamnati ba ta karkatar da dukiyar talakawa ba.”
Shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

KU KARANTA: A fito ayi bayani a kan N5,000 da za a raba wa 'yan Najeriya - SERAP

“Nuku-nuku da rashin fitowar jama’a su bibiyi kudin da aka dauka daga CBN bai dace ba. Kin yin hakan ya saba wa dokar kasashen waje, kuma cin amana ne.”

Ba a sa ranar da za a soma shari’a ba tukuna

A wannan kara mai lamba, FHC/ABJ/CS/559/2021, jaridar Punch ta ce ana so ayi bayanin tarihin duk kudin da aka karbi aro daga CBN tun daga 1999 zuwa 2015.

Sauran wadanda aka hada a karar sun hada da Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed, gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Kawo yanzu ba a sa ranar da za a saurari wannan kara ba. Lauyoyin da su ka shigar da karar a madadin SERAP su ne Kolawole Oluwadare da Adelanke Aremo.

A watan da ya gabata, labari ya zo maku cewa Kungiyar SERAP ta sake shiga kotu da Shugaba Buhari, wannan karo a kan haramta Twitter da aka yi a Najeriya.

A karar da kungiyar ta shigar, ta bukaci a taka wa shugaban kasa, NBC, da Lai Mohammed burki wajen hana amfani da manhajar sada zumuntan na zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel