Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya bace a sararin samaniyar kasar Rasha

Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya bace a sararin samaniyar kasar Rasha

  • An nemi jirgin sama an rasa a kasar Rasha
  • Rahotanni sun bayyana cewa da alamun jirgin ya fadi cikin teku
  • An tsinci barbashin wani jirgi amma babu tabbas jirgin AN-26 ne

Wani jirgin AN-26 na kasar Rasha mai dauke da akalla mutum 28 ya bace a yankin Kamchatka dake gabashin kasar Rasha, kafafen yada labaran sun ruwaito hukumomi da fada.

Jami'an gwamnatin kasar sun bayyana cewa jirgin na hanyar Petropavlovsk-Kamchatsky ne aka daina samun labarinsa, Aljazeera ta hakaito ranar Talata.

Rahotanni mabanbanta na magana kan abinda ya haddasa bacewar, inda wata majiya ta bayyanawa TASS cewa da yiwuwan jirgin ya fada cikin teku yayinda wata majiyar daban ta bayyanawa Interfax cewa jirgin ya fadi kusa da garin Palana.

An kaddamar da bincike na gaggawa domin nemo jirgin, cewar rahotanni.

DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya

Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya bace a sararin samaniyar kasar Rasha
Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya bace a sararin samaniyar kasar Rasha
Asali: Original

KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

Dan majalisa daya tilo da yaki fita daga PDP a Zamfara

Honarabul Salihu Usman Zurmi wanda ake kira Gurgu, shi kadai ne ya rage a cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar dokokin jihar Zamfara.

BBC Hausa ta yi hira da Salihu Usman Zurmi, domin jin abin da ya sa ya ki shiga jirgin APC.

Ganin irin alherin da PDP ta yi masa, ta ba shi tikitin shiga takara, don haka Salihu Usman Zurmi mai wakiltar mazabar Zurmi ta gabas, ya ki bin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel