Dakarun Sojojin Najeriya sun damke masu kaiwa yan Boko Haram makamai

Dakarun Sojojin Najeriya sun damke masu kaiwa yan Boko Haram makamai

  • Sojojin sun hallaka yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Dakarun Sojin sun damke masu kaiwa yan ta'adda abinci da makamai
  • Shugaban hafsan Soji ya yi kira ga Sojojin kada su ragawa yan ta'adda

Dakarun Sojin 195 Battalion, Sakta 1 Operation Hadin Kai, tare da jami'an sa kai CJTF sun samu nasarar damke masu kaiwa yan ta'addan Boko Haram makamai da kayayyaki.

Diraktan yada labaran hukumar, Onyeama Nwachukwu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata kuma Legit ta samu.

Ya bayyana cewa an damke makamai da kayayyakin da aka nufi kaiwa yan ta'addan bayan asarar da sukayi ranar 3 ga Yuli, 2021.

Onyeama ya bayyana cewa:

"Abubuwan da aka kwato daga wajen yan ta'addan BHT sun hada da gurnet daya, adda 1, mota daya, kekuna biyar, wayoyi biyu (Techno da Infinix) da kuma man fetur."
"Hakazalika sun kwato kwayoyin kara karfin maza, magungunan sauro, kayan masarufi, dss."

Bayan damke su, Sojoji sun gano sansanonin yan ta'adda kuma sun lalata su.

Hakazalika sun yi arangama da wasu yan ta'adda a kauyen Labe kuma suka hallakasu.

DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya

Dakarun Sojojin Najeriya
Dakarun Sojojin Najeriya sun damke masu kaiwa yan Boko Haram makamai HOto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci Soji su ceto wadanda aka sace

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji, 'yan sanda da sauran hukumOmin tsaro da su tabbatar da gaggauta ceto dukkan wadanda aka sace.

Buhari ya bada wannan umarnin ne a ranar Litinin ta wata takarda da Garba Shehu ya fitar a Facebook inda ya nuna damuwarsa kan harin jihohin Kaduna da na Neja wanda yace duk dalibai aka kwashe.

A yayin tabbatar da ci gaba da tura karin jami'ai dukkan yankunan da ke da matsala, shugaban kasan yayi kira ga hukumomin tsaron da su yi aikin gaggawa wurin ceto dukkan 'yan makarantan a jihohin tare da dawo dasu gida lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng