Zaben 2023: Tsohon Tauraron Super Eagles ya na goyon bayan Gwamna Yahaya Bello

Zaben 2023: Tsohon Tauraron Super Eagles ya na goyon bayan Gwamna Yahaya Bello

  • John Mikel Obi ya kai wa Yahaya Bello ziyara a gidansa da ke garin Abuja
  • Tsohon ‘Dan kwallon na Chelsea ya ce yana nan duk inda Bello ya sa gaba
  • Yahaya Bello ya ji dadin haduwarsa da Obi, ya yi magana a shafin Facebook

Tsohon shugaban ‘yan wasan kungiyar kwallon kafan Najeriya na Super Eagles, Mikel Obi, ya hadu da gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Mai girma gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya tabbatar da wannan a kan shafinsa na Facebook.

Bello ya rubuta a shafinsa, ya na cewa tauraruwar matasa za ta haska da kyau nan gaba. Tuni dai mutane su ka shiga maidawa gwamnan martani.

KU KARANTA: Masu goyon bayan takarar Bola Tinubu sun shigo Birnin Tarayya

“Yau na zauna da ‘danuwana, abokina, Mikel John Obi, tsohon ‘dan wasan Super Eagles, wanda ya taba cin gasar kofin Turai, Firimiya, kofin FA da AFCON, kuma ya samu zinari a gasar U-17 na Duniya.”

Mikel Obi ya nuna cewa ya na goyon bayan duk wata takara da Yahaya Bello zai yi nan gaba. Obi ya zauna da gwamnan ne a gidansa da ke garin Abuja.

‘Dan wasan kwallon kafan ya yabi gwamna Yahaya Bello yayin da suka hadu a ranar Lahadi, ya ce “Na ji duk abin da ake fada, kuma ake rubutawa a kansa.”

Tsohon ‘dan wasan na kugiyar Chelsea yake cewa gwamnan “shi ne wanda zai jagoranci matasa’, ya yi kira gare shi ya taimakawa masu tasowa a halin yanzu.

KU KARANTA: Gwamnatin Zulum yi ayyuka fiye da 500 a shekaru biyu a Borno

Zaben 2023: Tsohon Tauraron Super Eagles ya na goyon bayan Gwamna Yahaya Bello
Mikel Obi da Yahaya Bello Hoto: OfficialGYBKogi
Asali: Facebook

“Karin daraja ce gare ni in hadu da Mai girma gwamna da kansa, bayan duk abubuwan kirkin da na ji, kuma na karata a game da shi, daga ko ina a Najeriya.”

Obi yake cewa dalilin haduwansa da Alhaji Bello shi ne ya gode masa kan abubuwan da yake yi, ya kuma mara masa baya a kan duk wata takara da zai sa gaba.

Jaridar The Cable ta rahoto Obi yana cewa: “Babu wanda ya fi dacewa ya jagoranci matasa sai shi, ya na ta yin abubuwan kirki shi ya sa na kawo masa ziyara.”

Punch ta ce ziyarar ta zo ne a lokacin da gwamnan yake ikirarin mutanen Najeriya suna kiransa ya fito ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Bello ya bayyana haka a taron Masoyan Yahaya Bello a karkashin 'South-West Benefit Conference and a non-partisan group, Afenifere for Collective Transformation'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng