Magana ta yi karfi: Kungiyar Biyafara ta shirya kai Buhari gaban kotun Duniya a kan Kanu da Igboho
- MASSOB ta ce za a yi shari’a da Gwamnatin Muhammadu Buhari a kotu
- Kungiyar ta fitar da jawabi, ta ce ta gama shirin kai kara gaban kotun ICC
- Ana zargin Gwamnatin Najeriya da murkushe masu kururuwar barka kasa
Kungiyar Movement for the Actualization of the Sovereign State of Biafra watau MASSOB ta ce ta gama shirin zuwa kotu da shugaba Muhammadu Buhari.
Wannan kungiya mai rajin kafa kasar Biyafara mai ‘yancin kanta a Najeriya ta na kokarin zuwa kotu da shugaban kasar Najeriya ne a dalilin Nnamdi Kanu.
Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar 4 ga watan Yuli, 2021, kungiyar ta na zargin gwamnatin tarayya ne da murkushe magoya-bayan Biyafara.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta dade ta na neman Shugaban IPOB, Kanu - Lai
Daily Post ta ce wannan ya sa kungiyar ta MASSOB ta ce za ta kai shugaba Muhammadu Buhari gaban kotun ICC da ake hukunta manyan masu laifin Duniya.
UN, USA, G8 su taimaka mana - MASSOB
A wani jawabi da MASSOB ta fitar ta bakin darektan yada labaranta na kasa, Edeson Samuel, ta yi kira ga manyan Duniya su ceci duk masu kiran a raba Najeriya.
Kwamred Edeson Samuel ya roki majalisar dinkin Duniya, kasar Amurka, manyan kasashen Duniya takwas, da kungiyoyin kare hakki su kawo masu agaji.
“Tabargazar da gwamnatin tarayya ta ke yi, ya kai ga kashe-kashe, kama mutane ba tare da hakki ba, tsare jama’a, da azabtar da daruruwan masu fafutukar samar da kasar Biyafara, daga cikinsu har da Nnamdi Kanu.”
KU KARANTA: Siyasa: ‘Yan Majalisan Kwara sun yi wa Ministan Najeriya raddi
"MASSOB ta kammala shirye-shiryenta, ta hannun lauyoyinta na kai karar gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta zuwa kotun ICC Hague."
“MASSOB ta na gargadi cewa ka da wani mugun abu ya faru ga Mazi Nnamdi Kanu, Sunday Igboho da duk masu fafutukar samar da Biyafara da Oduduwa.”
A cewar kungiyar, an tsare wadannan mutane ana gallaza masu azaba, an hana su ganin likita.
Kwanakin baya kun ji cewa Barista Deji Enisenyin ya shigar da karar shugaba Muhammadu Buhari a kotu, a kan yawan fita kasashen waje da yake yi ganin likita.
Deji Enisenyin ya je kotu ya na so a haramta fita waje da Shugaban Najeriya ya ke yi. Lauyan ya ce Muhammadu Buhari ya na saba dokar kiwon lafiya da aka kawo a 2014.
Asali: Legit.ng