Kundin tsarin mulki ya dora wa Buhari nauyin murkushe Kanu da Igboho - Mataimakin Shugaban Kungiyar Lauyoyi

Kundin tsarin mulki ya dora wa Buhari nauyin murkushe Kanu da Igboho - Mataimakin Shugaban Kungiyar Lauyoyi

  • Kundin tsarin mulki ya dora wa Shugaba Buhari nauyin ya murkushe duk masu neman kafa kasa daga Najeriya, a cewar lauya
  • Lauyan ya ce akwai banbamci tsakanin fafutikar Tompolo da na su Kanu da Igboho da kuma Boko Haram a daya gefen
  • Ya ce babu Shugaban Kasar da zai nade hannu yana kallon ire-iren masu neman ballewar

Mataimaki na farko na Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) John Aikpokpo-Martins, ya fada cewar kundin tsarin mulkin Najeriyar ya wajabta wa kowane Shugaban Kasa murkushe dukkanin masu fafutikar ballewa kamar Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho.

Mista Aikpokpo-Martins ya ce karkashin dokokin Najeriyar neman ballewar abu ne da ya saba da kundin tsarin mulkin kasar.

Ya musanta ikirarin masu neman ballewar cewa neman kafa kasarsu ‘yancin dan Adam ne inda ya ce Sashe na 4 na cikin kundin tsarin mulki na 1999 (karkashin ‘yancin dan Adam) bai kunsar da batun neman raba kasa ba.

Jami’in kungiyar lauyoyin ya bayyana hakan a ra’ayin kashin kansa wanda ya wallafa a shafin Facebook a ranar Asabar.

Ya fara rubuta ra’ayin nasa da banbamce fafutikar da tsohon jagoran tsagerun yankin Neja Delta Government Ekpemupolo, da aka fi sani da Tompolo da kuma a daya gefen fafutikar da kungiyar Boko Haram da IPOB da kuma Igboho suke yi a daya gefen.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Lauyoyi
Kundin tsarin mulki ya dora wa Buhari nauyin murkushe Kanu da Igboho - Mataimakin Shugaban Kungiyar Lauyoyi

Da yake kafa hujjar matakin da gwamnatin ta dauka cewa yana kan doka kwararren lauyan ya ce:

“Ya kamata fa a sani cewa da akwai banbamci karara a tsakanin fafutikar da tsagerun yankin Neja Delta karkashin jagorancin actions Tompolo da sauransu suka yi da wadanda kungiyoyin Boko Haram da IPOB da Sunday Igboho suke yi a yanzu.
“Tompolo bai taba yin fafutikar neman kafa wata kasa ta daban; wannan yana muhimmanci kuma dole a yi waiwayen yadda aka tunkare shi.
“A bangaren Boko Haram da IPOB da Sunday Igboho dukkanin union suna fafutikar kafa kasashe ne daga cikin Najeriyar, Tompolo kuwa bai taba yin hakan ba; dan Najeriya ne da yake rajin samar da adalci da daidaito a matsayinsa na dan Najeriya kuma mazaunin kasar.
“Bisa tanadin kundin mulki babu wani Shugaban Kasa (Ya Allah Buhari ne ko Nnamdi ko Babatunde ko Ahmed ko Osahon ko Wike ko Aper, kai ko ma wane ne) da ya rike aikinsa da muhimmanci zai yi soko-soko da batun masu neman ballewar; tsarin mulki kuma doka ta ba shi damar da lallai ya murkushe wadannan mutanen.

Mista Kanu, wanda shi ne jagoran kungiyar IPOB yana kiran samar da kasar Biafra daga cikin Najeriyar, an gurfanar da shi gaban Kotun Tarayya a Abuja ranar Talatar makon jiya, kwana biyu bayan kama shi a wata kasar da ba a bayyana ba.

Wani ayarin jami’an tsaron hadin gwiwa ya kai samame kan gidan Mista Igboho a unguwar Soka, da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo da talatainin daren Alhamis; akalla sa’o’i 72 gabanin wani macin da ya shirya gudanarwa a Legas domin ci gaba da kiran kafa kasar Yarbawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel