‘Yan Majalisa sun dauki bangare a rigimar APC a Kwara, sun kai karar Minista gaban NWC
- Ana rikici tsakanin Lai Mohammed da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq
- Ministan yada labaran kasar ya samu sabani da Gwamnan jihar Kwara a APC
- ‘Yan majalisar jiha sun ce su na tare da Gwamna a wannan rigima da aka yi
‘Yan majalisar dokokin jihar Kwara sun yi watsi da ikirarin da Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, yake yi na cewa shi ya ba su kudin kamfe.
‘Yan majalisar dokoki su na tare da Gwamna
Jaridar Punch ta rahoto ‘yan majalisar suna maida wa Alhaji Lai Mohammed martani, sannan su kayi watsi da maganar da yake yi a kan zaben jam’iyya.
Wadannan ‘yan majalisa sun hakikance a kan cewa za a gudanar da zaben shugabanni a jiha a ranar 24 ga watan Yuli, 2021, kamar yadda APC ta tsara.
KU KARANTA: Za a kawo manhajar da za ta maye gurbin Twitter - Lai
Rahoton ya ce ‘yan majalisar dokokin sun yi wannan bayani ne yayin da su ka zanta da manema labarai a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuli, 2021, a garin Ilorin.
‘Yan majalisa 20 ne su ka halarci wannan zama da aka yi jiya kamar yadda mu ka samu labari.
Shugaban majalisar dokokin jihar Kwara, Hon. Yakubu Danladi-Salihu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Hon. Raphael Adetiba, shi ne ya gabatar jawabi.
Yakubu Danladi-Salihu ya ce Ministan labarai da al’adun bai cikin shugabannin APC na jihar Kwara, domin haka ba zai iya magana a madadin jam’iyya ba.
KU KARANTA: Sanata Kabiru Marafa ya ce dawowar Matawalle APC ba ta halatta ba
Daily Trust ta rahoto Danladi-Salihu ya na cewa ba za a koma zamanin siyasar uban gida ba. Su ka ce gwamna ne ya dauki dawainiyarsu a 2019, ba Ministan ba.
‘Yan Majalisa sun kai karar Lai Mohammed
“Bayanin da mu ka samu daga gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, wanda shi ne jagoran jam’iyya a Kwara, shi ne za a gudanar da zabe a ranar 24 ga watan Yuli kamar yadda za ayi a sauran jihohi.”
“Ya kamata jam’iyya ta hukunta Lai Mohammed na bada bayanin da ba daidai ba ga ‘ya ‘yan APC."
Haka zalika APC ta jiha, ta na tunanin a hukunta Ministan a kan bude ofishin ‘yan taware da ya yi a garin Ilorin, da nufin ya yaki gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
A makon da ya gabata kun samu labari Ministan labarai na kasa, Lai Mohammed, ya ce Gwamnatin tarayya ta dade ta na neman Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
Lai Mohammed yake cewa Mazi Nnamdi Kanu ya na zama a katafarorin gidaje, ya na yawo a jiragen sama, sannan ya na sa tufafi masu tsada na a-zo-a-gani a waje.
Asali: Legit.ng