Bamu da hannu cikin kisan 'yar budurwa a filin zanga-zanga

Bamu da hannu cikin kisan 'yar budurwa a filin zanga-zanga

  • Yan sanda sun nesanta kansu da mutuwar budurwa a filin zanga-zanga
  • Jami'an sunce ko sau guda basu harba harsashi ba
  • Bayan dubi cikin gawar, sun ce da alamun caka mata wuka akayi

Hukumar yan sandan jihar Legas ta yi watsi da rahotannin cewa jami'ai hukumar suka harbe yar budurwar da ta mutu a filin zanga-zangan masu rajin kafa kasar Yarbawa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a jawabin da Kakakin hukumar, Olamuyiwa Adejobi, ya saki, rahoton Punch.

Ya ce kawai ana kokarin tayar da hankalin jama'a ne saboda ko sau guda yan sanda basu harba harsashi ba.

Yace:

"Jami'an hukumar basu harba ko harsashi guda ba. Gawar yarinyar da aka tsinta a wuri mai nisa da Ojota inda akayi zangan-zangan.. da bushesshen jini dake nuna cewa ba sabon gawa bace."
"Bayan dubi cikin gawar, an ga ciwo dake da alaman suka da abu mai kaifi."
"Wannan labarin karya ce. Saboda haka hukumar na kira ga jama'a suyi watsi da labarin kuma su cigaba da harkokin gabansu.

DUBA NAN: Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa

Bamu da hannu cikin kisan 'yar budurwa a filin zanga-zanga
Bamu da hannu cikin kisan 'yar budurwa a filin zanga-zanga
Asali: UGC

KU KARANTA: Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki

Wata mata ta kuka kan barkonon tsohuwa

Bayan hotunan gawar yarinyar, bidiyo ya yadu na wata mata dake kuka kan yadda barkonon tsohuwa ya kusa hallakata da 'yayanta cikin gidansu.

Matar ta nuna tukunyar barkonon da ya shiga gidanta.

Tace: "Sun son kasheni. Ina da kananan yara. Kalli barkonin hayakin da aka jefo gidan tun daga Abiola Garden."

Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda

Rikici ya rincabe a yankin Ojota na jihar Legas yayin da masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa suka bijirewa umarnin 'yan sanda suka fara zanga-zanga.

Duk da 'yan sanda da sojoji sun mamaye wurin zanga-zangar a sa'o'in farko na yau Asabar, masu zanga-zangar daga bisani sun tsinkayi wurin.

Amma kuma jami'an tsaro dauke da bindigogi sun yi kokarin hana su zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel