An bindige 'yar budurwa mai talle a wajen taron zanga-zangan masu neman kasar Yarabawa

An bindige 'yar budurwa mai talle a wajen taron zanga-zangan masu neman kasar Yarabawa

  • Duk da harin da DSS ta kaiwa Sunday Igboho, matasa sun yi zanga-zangar da ya shirya
  • Jami'an yan sanda sun tarwasa matasan da suka fito zanga-zangar
  • Wannan ya biyo bayan simamen da jami'an tsaro suka kai gidan mai rajin kafa kasar Yarabawa

An hallaka wata 'yar budurwa mai kasa da shekaru 20 a unguwar Ojota, jihar Legas, yayinda yan sanda ke kokarin tarwatsa masu zanga-zanga ranar Asabar.

A cewar mazaunan yankin, harsashi ya samu yarinyar ne yayinda yan sanda suka fara harbi.

Masu idanuwan shaida sun bayyana sunan budurwar matsayin Jumoke, rahoton DT.

Sun ce ta fito tallan lemun kwalba kamar yadda ta saba amma ta gamu da ajalinta.

Mutane sun tafi da gawarta.

DUBA NAN: Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa

An bindige 'yar budurwa mai talle a wajen taron zanga-zangan masu neman kasar Yarabawa
An bindige 'yar budurwa mai talle a wajen taron zanga-zangan masu neman kasar Yarabawa
Asali: Original

KU KARANTA: Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki

Rikici ya rincabe a Legas bayan masu son kafa kasar Yarabawa sun bijirewa 'yan sanda

Rikici ya rincabe a yankin Ojota na jihar Legas yayin da masu zanga-zangar kafa kasar Yarabawa suka bijirewa umarnin 'yan sanda suka fara zanga-zanga.

Duk da 'yan sanda da sojoji sun mamaye wurin zanga-zangar a sa'o'in farko na yau Asabar, masu zanga-zangar daga bisani sun tsinkayi wurin.

Amma kuma jami'an tsaro dauke da bindigogi sun yi kokarin hana su zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng