NNPC ta sa ranar da za a fara gyaran matatun mai da za su cinye Naira Biliyan 570

NNPC ta sa ranar da za a fara gyaran matatun mai da za su cinye Naira Biliyan 570

  • Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari ya ce za a fara gyara matatun danyen mai
  • Ana sa ran nan da farkon 2023 a kammala aiki a matatun Warri da Kaduna
  • Za a shafe fiye da shekaru uku kafin a karkare gyara matatar da ke Fatakwal

Daga wannan wata da aka shiga na Yulin 2021 ne kamfanin NNPC na kasa zai fara aikin gyaran matatun danyen man da ke garin Kaduna da Warri.

Jaridar Daily Trust ta ce a daidai wannan lokaci ne kuma ake sa ran a soma tace danyen mai a matatun gwamnati da ke garin Fatawal, jihar Ribas.

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari, ya bayyana wannan da aka yi hira da shi a Arise TV.

KU KARANTA: Gwamnati za ta saye hannun jari a kamfanin Dangote - NNPC

A watan Yulin nan za a soma aiki

Za a bada kwangilar gyaran matatun Kaduna da na Warri a watan Yuli, a gama a daidai lokacin da za a soma tace danyen mai a a matatar da ke Fatakwal.”

Malam Mele Kolo Kyari ya ce za a shafe watanni 40 ana gyaran matatar garin Fatakwal, amma bayan shekara daya da rabi za a iya fara tace danyen mai.

Kamar yadda jaridar Sun ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, 2021, Najeriya za ta fara tace danyen mai a gida a cikin watan Junairun 2023.

A halin yanzu ana fita da danyen mai daga kasar ne zuwa matatun ketare, a dawo da fetur Najeriya.

Shugaban NNPC
GMD NNPC, Mele Kyari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: NNPC za ta ci bashi domin mallaka 20% a matatar Dangote

Lokacin da majalisar zartarwa ta kasa watau FEC ta amince da wannan aiki da zai ci Dala miliyan 1.5 (kusan Naira biliyan 570), an yi ta surutai a kasar.

Abin da ke shiga asusun FAAC ya ragu

A game da asarar da NNPC da gwamnatin tarayya su ke yi yanzu, Mele Kyari ya bayyana cewa hakan ya na rage abin da kamfanin ta ke zuba wa asusun FAAC.

“Ya kamata mu rika zuba Naira biliyan 120 a asusun hadaka na gwamnati a kowane wata, amma a watanni hudun da su ka wuce mun gagara yin haka.”
“Amma ba wai ba mu zuba ko sisi ba ne kamar yadda ake fada, a watan Yuni mun jefa Naira biliyan 38 ”

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta yi kasafin Naira Biliyan 900 domin a biya kudin tallafin mai a 2022. Sai Najeriya ta kashe kusan Tiriliyan 1 domin mai ya yi sauki.

Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce wadannan kudi sun yi yawa sosai, ta fara duba yiwuwar a kara farashin fetur, ayi wasu abubuwan da wannan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel