Buhari zai iya cigaba da biyan tallafin mai, ya ware N900bn saboda a hana fetur tashi a 2022
- Gwamnatin Tarayya ta ware N900bn domin biyan tallafin mai a shekarar 2022
- Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta ce wadannan kudi sun yi yawa sosai
- Ahmed ta fara duba yiwuwar a kara farashin fetur, ayi wasu abubuwa da kudin
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta na tunanin kashe kudi har Naira biliyan 900 a shekara mai zuwa domin biyan tallafin man fetur.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi kasafin Naira tiriliyan 13.91 na shekarar badi.
Ministar kudi, kasafi, da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta bayyana wa ‘yan jarida wannan yayin da ta ke bayani kan TEF/FSP na 2022-2024.
KU KARANTA: Tsofaffin Ma’aikatan Gwamnati za su karbi fanshonsu – PenCom
Gwamnati Tarayya ta yi kasafin N13.91tr a shekarar badi
Zainab Ahmed ta ce kasafin kudin shekara mai zuwa zai samu gibin 3.05%. Abin da aka yi kasafi na 2022, ya zarce kudin da aka ware za a kashe a shekarar nan.
“Iyakar kasafin kudin N11.09tr ne, amma idan aka hada da wasu abubuwa, za a samu N13.91tr. A shekarar 2023, za ayi kasafin N15.45tr, sai N16.77tr a 2024.”
Tallafin man fetur zai lashe Naira biliyan 900 a shekara
The Nation ta rahoto Ministar tattalin arzikin ta na cewa gwamnatin tarayya za ta iya kashe Naira biliyan 900 wajen biyan tallafin fetur a shekara mai zuwa.
Ahmed ta ce muddin gwamnatin tarayya ta cigaba da saida fetur da araha, za a kashe wannan kudi.
KU KARANTA: Hisbah za ta rushe duk mutum-mutumin da ke kasuwannin Kano
“Dole mu yi watsi da wannan tsari na tallafin man fetur domin Najeriya ta na saida wa duka kasashen yankin nan mai ne da araha kurum.”
“Farashin fetur ya kai $500 a wasu kasashen Afrika.”
“Akwai tsirarun mutane a Najeriya da za su iya hawa mota, wasu suna da motoci biyu. Talakan da ya kamata a ba tallafi, motar haya yake amfani da ita. Saboda haka tallafin bai yi masa wani amfani.”
Ministar ta ce ana tunanin kawo hanyoyi da za su rage radadi idan an janye tallafin man.
“Abin da wahala, amma dole mu janye wannan kudi. Makarantu nawa za a iya gina wa, dakunan shan magani nawa za a gina (da N900bn)? Ba dabara ba ce."
Asali: Legit.ng