Jam’iyyar PDP za ta kai karar Matawalle a Kotu saboda komawa APC, ta nemo manyan Lauyoyi

Jam’iyyar PDP za ta kai karar Matawalle a Kotu saboda komawa APC, ta nemo manyan Lauyoyi

  • Jam’iyyar adawa ta na shirin kai karar Gwamnan Zamfara a gaban Kotu
  • PDP ta dauko lauyoyin da za su tsaya mata tsakaninta da Bello Matawalle
  • Matawalle ya tsere zuwa APC ne bayan ya zama Gwamna da kuri’un PDP

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta fara magana da wasu manyan lauyoyi biyar da za su kare ta a kotu, inda za ta kalubalanci gwamnan Zamfara, Bello Matawalle.

Jaridar Punch ta ce babbar jam’iyyar adawar za ta kai karar gwamna Bello Matawalle kotu, saboda ya sauya-sheka, ya koma APC mai mulki a makon nan.

Wani daga cikin ‘yan majalisar aiwatar wa na PDP, ya shaida wa jaridar a ranar Alhamis cewa jam’iyyar adawar ra na tattara takardun da za ta shiga kotu da su.

KU KARANTA: Har gobe ana nan ana yin rashin adalci a PDP - Buba Galadima

SANs za su tsayawa PDP a kotu ba tare da an biya su ba

Wannan jigo a jam’iyyar adawa, wanda ya na cikin ‘yan majalisar NWC ta Prince Uche Secondus, ya ce lauyoyin za su tsaya masu ne ba tare da an biya su kudi ba.

Da yake magana ba tare da ya bari an bayyana sunansa ba, jami’in na PDP ya nuna akwai bukatar a gabatar da wannan kara domin shari’a ta raba masu gardama.

“Manyan lauyoyi da su ka kai matsayin SAN biyar mu ka tuntuba, kuma sun shirya kare mu a gaban kotu kyauta domin a ceto damukaradiyyar kasar nan.”

Har ila yau, majiyar ta shaida wa manema labaran cewa wannan kara ta na da muhimmanci sosai domin za ta warware sababbin matsaloli a shari’ar siyasar Najeriya.

Bello Matawalle a APC
Bello Matawalle ya koma APC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Matawalle zai gane bai da wayau a 2023 - 'Dan Majalisa

“Nan da ba dade wa ba, za ku ji daga gare mu.”

Gwamna Bello Matawalle wanda ya koma APC mai mulki a ranar Talata zai fuskanci kalubale a kotu domin ta hanyar shari’a ne ya samu damar darewa kujera.

A zaben gwamnan jihar Zamfara da aka yi a 2019, Matawalle ya zo na biyu, amma kotu ta ba shi nasara saboda APC da ta fi kuri’u ba ta yi zaben fitar da gwani ba.

A yau ne mu ka samu labari cewa zaman tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a PDP ya gagara yiwuwa, ya na hangen komawa APC da ya bari a 2014.

Sanata Kwankwaso ya zauna da wasu manyan APC, ya na tunanin barin PDP. Gwamnan Zamfara ya na cikin masu ba shi shawarar ya fice daga jam'iyyar adawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel