Sunday Igboho ya nemi alfarma daga wurin Rundunar 'Yan Sanda gabanin gangamin Legas

Sunday Igboho ya nemi alfarma daga wurin Rundunar 'Yan Sanda gabanin gangamin Legas

  • Igboho ya ce ba gudu ba ja da baya wajen gabatar da gangamin da suka shirya a Lagos 3 ga Yuli
  • Ya ce ya na rokon kwamishinan yan sandan Lagos da ya bada kariya ga mahalarta gangamin saboda gangamin lumana ne
  • Za'a fara gudanar da gangamin daga unguwa Ojota da misalin karfe 9 na safe

Dan gwagwarmayar Yarbawa, Mr Sunday Adeyemo Igboho, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya karyata labarin dage taron gangamin da ya shirya a Lagos ya kuma roki rundunar yan sanda ta basu kariya, Daily Trust ta ruwaito.

Ana cikin fargaba a gaba daya jihar sakamakon gangamin.

Mr Sunday Igboho
Dan gwagwarmayar Yarbawa, Mr Sunday Igboho. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

Da safiyar Laraba, an samu rahoton dage gangamin har sai baba ta gani kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Amma Igboho, wanda shi ne jagora, ya karyata labarin kuma ya bukaci yan sanda su bada kariya ga wanda za su halarta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Olayomi Koiki, ya fitar Igboho ya ce, "muna sanar da daukacin al'umma cewa zamu gabatar da taron gangamin mu na Jihar Lagos zai gudana ranar Asabar 3 ga watan Yuli, 2021 kamar yadda aka tsara
"Muna amfani da wannan damar mu roki kwamishinan 'yan sanda na Jihar Lagos da ya tsare dukkanin Yarabawa da za su zo taron gangamin da wanda zasu shigo jihar saboda mutanen da zasu yi yunkurin kawo cikas ga gangamin lumanar.

KU KARANTA: Mafarauta sun ɗirka wa mai garkuwa harsashi ya mutu yayin da yazo karɓar kuɗin fansa

"Chief Sunday Igboho ba zai iya dakatar da gangamin ba saboda duka Yarabawa ne ke so kuma sun fi shi iko.
"Gangamin zai fara a Ojota da misalin 9:00 na safe.

Nnamdi Kanu na samun goyon bayan dillalan makamai na ƙasashen waje, Dattawan Arewa

A wani labarin, kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi takatsantsan da lamarin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, rahoton Daily Sun.

A cewar kungiyar ta Arewa, shugaban na masu fafutikan kafa kasar Biafra yana da abokan hulda sosai a kasashen ketare.

Kungiyar ta yi wannan furucin ne yayin da ta ke martani kan sake kama shugaban na IPOB a ranar Talata 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel