Gwamnatin Buhari za ta sake gurfanar da Nnamdi Kanu a kotu da laifin kisan mutane barkatai

Gwamnatin Buhari za ta sake gurfanar da Nnamdi Kanu a kotu da laifin kisan mutane barkatai

  • Gwamnatin Tarayya ta na shirin gurfanar da Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
  • Lauyoyin Gwamnati za su jefi Kanu da wasu zargin na dabam wannan karon
  • Za a tuhumi wanda ake zargin da laifin mutuwar mutane da yawa a Najeriya

Jaridar This Day ta ce Gwamnatin tarayya ta na kokarin dauko lauyoyi da za su gurfanar da shugaban haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Hukumomin Najeriya sun yi ram da Mazi Nnamdi Kanu a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa, a ranar Juma’ar da ta gabata, 24 ga watan Yuni, 2021.

Jaridar ta fahimci cewa a daren jiya wasu jami’an ma’aikatar shari’a na tarayya su na tattaro kwararrun lauyoyi da za su tafi gaban kotu da Nnamdi Kanu.

KU KARANTA: Wadanda su ke ba IPOB gudumawa sun shiga uku bayan cafke Kanu

Lauyoyin ma’aikatar shari’ar za su shigar da Kanu kotu ne a kan wasu sababbin zargi da ake yi masa, daga ciki har da hannu a wajen hallaka mutane da-dama.

Jami’an tsaro da hukumomin gwamnatin Najeriya su na da hujjoji masu karfi da za su gabatar domin nuna jagoran na IPOB ya haddasa kisan mutane rututu.

Zunuban Nnamdi Kanu a wajen shari'a

A cikin wadanda aka kashe a sakamakon hudubobin jagoran na kungiyar IPOB har da jami’an hukumar gudanar da zabe na INEC a jihohin Kudancin kasar nan.

Sannan ana zargin Kanu da laifi wajen kisan gillar da aka yi wa jami’an ‘yan sanda da ma’aikatan gidan yari a bangaren Kudu maso kudu da na Kudu maso gabas.

KU KARANTA: Ba za mu iya ceton ka ba - Birtaniyya ga Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu da Lauyoyi
Nnamdi Kanu a Kotu Hoto: www.dw.com
Asali: UGC

Wani jami’in tsaro ya shaida wa jaridar cewa suna da hujjojin da za su gabatar idan an je kotu;

“Mu na da dalilai masu karfi da ke nuna umarnin da ya rika ba yaran IPOB su kashe jami’an tsaro da wasu mutanen da ba su tare da fafutukarsa.”
“Akwai alaka ta kai-tsaye tsakanin sakonnin bidiyoyi da na sauti da kuma barnar da ake yi a Kudu maso gabas da ya kashe mutane fiye da 100.”

An ji cewa gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta sa ido kamfanin Dangote ya rika tace mai shi kadai ba, ba tare da ta yi tarayya da shi domin a tsare tattalin arzikin kasar.

Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce Aliko Dangote bai da sha’awar saida wa gwamnatin hannun jari a kamfaninsa da zai rika tace ganguna 650, 000 a kullum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel